Trends

Najeriya Na Asarar ₦5bn–₦8bn Duk Wata Sakamakon Raunin Grid – NISO

Hukumar Nigerian Independent System Operator (NISO) ta bayyana cewa Najeriya na asarar kuɗi tsakanin ₦5 biliyan zuwa ₦8 biliyan a kowane wata sakamakon gazawar tsarin isar da wutar lantarki (grid).

Babban Daraktan hukumar, Abdu Bello, ne ya bayyana hakan yayin bikin cika shekara guda da kafuwar NISO a Abuja.

Ya ce a lokacin fara aiki, asarar wutar lantarki ta kai kusan kashi 10%, amma yanzu ta ragu zuwa kashi 7.05%, tare da burin kaiwa tsakanin kashi 5 zuwa 6%.
Bello ya ce a cikin shekara guda da ta gabata, an mayar da hankali ne kan gina ingantacciyar hukuma, daidaita tsarin grid, da kuma aiwatar da gyare-gyaren kasuwar wutar lantarki.

Ya ce, “Ba kawai muna bikin cika shekara guda ba ne, muna kuma waiwayar irin ƙoƙarin da aka yi, ci gaban hukumomi, da tasirin da aka samu.”
Ya ƙara da cewa an kafa NISO ne a shekarar 2024 bayan raba ayyukan Transmission Company of Nigeria (TCN), domin kula da sarrafa tsarin wuta, gudanar da kasuwa, da kuma tabbatar da bin ƙa’idojin grid.

Daya daga cikin manyan nasarorin da ake kokarin samu shi ne sauya tsarin zuwa na zamani ta hanyar amfani da fasaha. Bello ya ce NISO na hanzarta girka tsarin SCADA da Energy Management Systems (EMS), da kuma kayan telemetry domin ba da damar sa ido kai tsaye da gudanar da kasuwa.

Ya kuma bayyana cewa hukumomin kula da harkokin wuta sun umarci kamfanonin rarraba wuta da su girka na’urorin IoT a kan layukan wuta, domin samar da cikakken bayani daga matakin samarwa zuwa rarrabawa.
Bello ya ce hakan zai ƙara inganta yadda ake sarrafa grid da kuma ingancin aiki.

Haka kuma, NISO na shirin gabatar da tsarin “grid islanding” domin kauce wa katsewar wuta a faɗin ƙasa baki ɗaya, tare da tilasta bin ƙa’idojin da suka shafi daidaiton mitar wuta.

Ya ƙara da cewa wasu kamfanonin samar da wuta sun riga sun fara inganta daidaiton grid ta hanyar amfani da tsarin “free-governor mode” wajen gudanar da ayyukansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *