Trends

Ireti Kingibe Ba Za Ta Koma Majalisar Dattawa ba 2 a 027 – Wike

Nyesom Wike Minista Birnin Tarayya

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya sake jaddada cewa Sanata Ireti Kingibe ba za ta koma Majalisar Dattawa a 2027 a matsayin wakiliyar FCT ba, yana mai danganta hakan da abin da ya kira rashin gamsasshen aiki da kuma rashin tasiri a ofis.

Wike ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a Abuja, inda ya ce bai ga isasshen sakamako daga ayyukan sanatar ba.

“Sanata Ireti Kingibe ba za ta dawo a matsayin sanatar FCT ba, kuma har yanzu ina nan kan bakana,” in ji shi.
Da yake mayar da martani kan zargin da Kingibe ta yi cewa ta yi ƙoƙarin tuntuɓarsa amma ba ta samu nasara ba, Wike ya musanta hakan.

“Ban ma san lambarta ba. Ni ba mutumin da ke yin riya ba ne. Na faɗa muku, ku rubuta yau — yau biyu ga watan Maris. Rahoton aikinku zai nuna. Me kika yi a matsayin sanata?” in ji ministan.

Wike ya jaddada cewa haɗin gwiwa a shugabanci ya kamata ya dogara ne kan sakamako a zahiri, ba wai kawai alaƙar siyasa ba.

Ya ƙara da cewa mayar da hankalinsa shi ne aiwatar da ayyukan da za su kasance a bayyane ga jama’a, musamman a garuruwan da ke wajen birnin Abuja da sauran al’ummomin FCT.

“Ina son zuwa garuruwan da ke wajen birni da al’ummomi domin mutane su ga abin da aka yi. Ba na nan domin cin zarafin kowa. Idan ana son zama abokina, ba dole ba ne. Ina son haɗin gwiwa, amma haɗin gwiwa kan me? Idan kai sanata ne, ka tabbata ka yi aiki da kyau. Bai kamata mu ɗauki ra’ayoyi da sauƙi ba,” in ji shi.