Gwamnatin Tarayya ta sanar da fara aiwatar da Dokar Shugaban Ƙasa ta 9 ta shekarar 2026, wadda ta tanadi cewa duk kuɗaɗen shiga daga man fetur za a riƙa tura su kai tsaye zuwa Asusun Kwamitin Raba Kuɗaɗen Tarayya (FAAC).
Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Harkokin Tattalin Arziƙi, Wale Edun, ne ya bayyana hakan bayan taron farko na kwamitin, yana mai cewa wannan mataki zai kawo gagarumin sauyi a yadda ake sarrafa kuɗaɗen da ake samu daga man fetur.
Wannan tsari ya yi daidai da umarnin Shugaba Bola Tinubu na tabbatar da cewa duk kuɗaɗen shiga na ƙasa suna bin tanadin kundin tsarin mulki, domin kare haƙƙin rabon kuɗaɗe ga matakai uku na gwamnati — tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi. An ce matakin zai inganta tsarin tattara kuɗaɗe tare da ƙara gaskiya da rikon amana a bangaren makamashi.
Ɗaya daga cikin muhimman sauye-sauyen da dokar ta kawo ya shafi kamfanin mai na ƙasa, NNPC Limited. A cewar Ministan, “NNPC Limited za ta daina, nan take, cire kashi 30 cikin 100 na kuɗin gudanarwa da kuma kashi 30 cikin 100 na kuɗin binciken sabbin rijiyoyin mai daga ribar man fetur da iskar gas a karkashin yarjejeniyoyin raba riba (Production Sharing Contracts).”
Haka kuma, gwamnati ta dakatar da wasu hanyoyin karkatar da kuɗaɗe zuwa wasu asusu. Edun ya ce, “An dakatar da tura duk kuɗaɗen tara na kone iskar gas (gas flare penalties) zuwa Asusun Midstream da Downstream na Gas (MDGIF) nan take, bisa ga tanadin dokar.”
Duk da cewa dokar ta umarci a riƙa biyan kuɗaɗe kai tsaye zuwa asusun tarayya, gwamnati ta bayyana cewa tana la’akari da yiwuwar tasirin da hakan ka iya yi wa kasuwa. Domin kauce wa rikicewa da kuma tabbatar da amincewar masu zuba jari, kwamitin ya amince da bayar da wani wa’adin sauyi ga kamfanoni domin su daidaita tsarin biyan kuɗaɗen ribar mai, kuɗin sarauta (royalty oil), da harajin mai (tax oil).
Game da wannan sauyi, Ministan ya ce, “Har sai kwamitin ya fitar da cikakkun ƙa’idoji, kamfanoni za su ci gaba da bin tsohon tsarin biyan kuɗaɗe.
A lokacin sauyin, kwamitin zai fitar da bayyanannun umarni da tsari guda domin tabbatar da sauyi cikin lumana.”
Domin sa ido kan aiwatar da wannan sauyi, an kafa wata ƙaramar kwamitin fasaha ƙarƙashin jagorancin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Makamashi.
An ɗora wa wannan ƙungiya alhakin tsara cikakkun ƙa’idojin sauyi cikin makonni uku, tare da duba Dokar Masana’antar Man Fetur (Petroleum Industry Act) domin magance duk wata tangarda ta fuskar kuɗi da ta ke akwai.
Edun ya sake jaddada aniyar gwamnati na tabbatar da gaskiya da riƙon amana, yana mai alƙawarin ci gaba da sanar da jama’a yadda aiwatar da dokar ke gudana.
Babban buri na wannan tsari shi ne tabbatar da cewa albarkatun man fetur na Nijeriya suna haifar da ainihin fa’ida mai auna tasiri ga al’ummar ƙasar a dukkan jihohi.
