Kamfanin jiragen sama na Ibom Air ya haramta wa wata fasinja, Misis Comfort Emmanson, yin tafiye-tafiye da duk wani jirgin kamfanin, bayan zargin ta da yi wa ma’aikatan jirgi da wani fasinja duka.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, bayan jirgin da ya taso daga Uyo ya isa filin jirgin sama na Lagos, inda Misis Emmanson ta kai wa waɗanda ta farmaka hari, bayan koke kan kin kashe wayarta yayin jirgi.
An ce ta taka ƙafafun wani fasinja, ta yage masa gashin wando (wig) da tabarau, ta jefa su ƙasa, sannan ta yi masa duka. Kamfanin ya kuma zarge ta da mare ma’aikatan jirgi da suka yi ƙoƙarin shiga tsakani, tare da yunƙurin amfani da ɗaya daga cikin bututun kashe gobara na jirgin a matsayin makami, lamarin da jami’an tsaron filin jirgi suka shawo kansa kafin a mika ta ga ‘yan sanda.
A cikin wata sanarwa da Aniekan Essienette, Manaja na Ƙungiyar a sashen Talla da Sadarwa ta sanya wa hannu a ranar Litinin a Uyo, Ibom Air ta bayyana cewa halayen Misis Emmanson sun zama barazana ga lafiyar ma’aikata, fasinjoji, da kuma jirgin, kuma hakan na iya janyo lalacewar jirgin, tana mai gargadin cewa ba za ta lamunta irin hakan ba.
“Ibom Air ta tabbatar cewa a ranar Lahadi, 10 ga Agusta 2025, wani lamari ya faru a cikin jirginmu na Uyo zuwa Lagos da ya shafi wata fasinja mai suna Misis Comfort Emmanson, wadda halayenta suka zama barazana ga lafiyar ma’aikatanmu, fasinjoji, da jirgin.
“Kafin tashi daga Uyo, an umarce ta bisa tsarin tsaron tashi jirgi da ta kashe wayarta. Ta ƙi yin hakan har sai da Kyaftin ya yi sanarwa, sannan wani fasinja da ke zaune kusa da ita ya karɓi wayar ya kashe.
“Wannan ya jawo tashin hankali daga gare ta. An samu kwantar da hankali, kuma jirgin ya tashi yadda aka tsara.
“Da isowa Lagos, ta jira kowa ya sauka sannan ta kai hari ga mai kula da fasinjoji (purser) wadda ta umarce ta a baya. Ta taka ƙafarta, ta yage mata wig, ta cire mata tabarau ta jefa ƙasa, sannan ta yi mata duka da takalminta.
“Ta mare ta sau da dama, kuma lokacin da wani ma’aikacin jirgi ya shiga tsakani, ta mare shi ma. Daga nan ta yunƙura ta kwace bututun kashe gobara don amfani da shi a matsayin makami, abin da zai iya lalata jirgin.
“A wannan lokaci, Kyaftin ya sanar da jami’an tsaro. Kafin isowarsu, mai kula da fasinjoji — kamar yadda aka gani

