Boss Mustapha Ya Musanta Jita-Jitar Barin APC Zuwa ADC

Boss Mustapha Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Boss Mustapha, ya karyata rahotannin da ke cewa ya bar jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar adawa ta African Democratic Congress (ADC), yana mai bayyana labarin a matsayin ƙarya tsagwaron (fake news).

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, Mustapha — wanda ya yi SGF daga 2017 zuwa 2023 a ƙarƙashin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari — ya bayyana cewa wannan zargi babu gaskiya a cikinsa, kuma bai taɓa yin wata tattaunawa da ‘yan adawa ko kawayensu ba.

“Hankalina ya kai kan wani labarin da ke yawo a kafafen yada labarai da ke haɗa sunana da wata haɗakar jam’iyyun adawa tare da zaben ADC a matsayin jam’iyyarsu. Wannan labari ƙarya ne. Ba ni cikin kowace haɗakar jam’iyyun adawa kuma ban taɓa tattaunawa da kowa daga cikinsu ba,” in ji shi.

Ya jaddada cewa har yanzu yana daga cikin manyan masu kafa APC tun asali, kuma ba shi da niyyar barin jam’iyyar da ya taimaka wajen kafa ta. Duk da ya amince cewa APC kamar kowace jam’iyyar siyasa na fuskantar ƙalubale, ya ce mafita ita ce a yi aiki daga ciki, ba ta hanyar guduwa ba.

Ya bukaci jama’a da su yi watsi da irin waɗannan jita-jita.

A watan Yuli da ya gabata, Mustapha ya kuma karyata ra’ayin da ke cewa mutum guda ne kaɗai ya jagoranci nasarar Buhari a zaben 2015, yana mai cewa tun kafin haɗewar jam’iyyun da suka kafa APC, Buhari na da fiye da ƙuri’u miliyan 12, yayin da haɗin gwiwar jam’iyyun ya ƙara masa ƙuri’u kusan miliyan uku ne kawai.

One thought on “Boss Mustapha Ya Musanta Jita-Jitar Barin APC Zuwa ADC

Comments are closed.