Trends

Gabas ta Tsakiya: Faransa za ta fara jefa kayan agaji ta sama a Gaza

Yankin Gaza da Yakin ya cinye

Faransa ta sanar da shirinta na aikewa da tan 40 na kayayyakin agajin jin ƙai ciki harda abinci zuwa Zirin Gaza ta hanyar jefosu ta sama, yayin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce wannan yanki da ke fuskantar ƙawanya na buƙatar agajin gaggawa.

Ministan harkokin wajen Faransa, Jean-Noel Barrot, yayin wata hira da manema labarai a gefen taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan makomar yankin Falasɗinu da Isra’ila, ya ce a ranar Juma’ar nan za a fara aikewa da ton 10 na kayayyakin abinci zuwa Gaza.

Ministan ya kuma bayyana cewa, ƙasarsa za ta yi wannan aiki ne tare da haɗin gwiwar ƙasar Jordan, wajen jigilar kayayyakin inda ake sa ran jirage huɗu ne za su yi wannan aikin.

Faransa dai ta bayyana cewa, akwai ton 52 na kayan abinci da aka hana shigar da su Gaza, wanda ƴan kilomita kalilan ne tsakaninsa da wannan yanki.

Ministan harkokin wajen ya kuma bayyana matakin ƙasarsa na shirin sanya hannu kan wata takarda da aka yi wa taken sakon New York, domin janyo hankalin sauran ƙasashe su mara mata bayaga fafutukar samar da ƙasashen Isra’ila da Falasɗinu.

A taron yini biyu da aka gudanar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, illahirin ƙasashe 125 da suka amsa kira sun yi amanar cewa hanya ɗaya tilo ta kawo ƙarshen rikicin Gaza ita ce samar da ƙasashe biyu halastattu.