Trends

Shugaban Masar Ya Yi Maraba Birtaniya na Goyon Bayan Ƙirƙirar Kasar Falasdinu

Shugaban Masar Abdel-Fattah al-Sisi

Shugaban ƙasar Masar, Abdel-Fattah al-Sisi, ya yi maraba da shawarar da Birtaniya ta ɗauka na shirin amincewa da kafa ƙasar Falasdinu a watan Satumba, idan Isra’ila ta ƙi amincewa da tsagaita wuta a Gaza.

Shugaba Sisi ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook a ranar Laraba, inda ya ce:
“Wannan mataki ne mai muhimmanci wajen inganta mafita ta ƙirƙirar ƙasashe biyu.”

Ya bayyana cewa yana yaba wa jawaban Firayim Ministan Birtaniya, Keir Starmer, dangane da niyyar ƙasarsa na amincewa da kafa ƙasar Falasdinu.

“Ina fatan Birtaniya za ta ɗauki wannan tarihi mataki cikin hanzari, ba tare da wani sharadi ko ƙuntatawa ba,” in ji Shugaban Masar.

Sisi ya sake jaddada matsayar da Masar ta dade da riƙe cewa mafita ta gaskiya da kuma cikakkiyar warware rikicin Falasdinu ita ce hanya ɗaya tilo da za ta samar da zaman lafiya mai ɗorewa a Gabas ta Tsakiya.

A ranar Talata, Firayim Ministan Birtaniya, Keir Starmer, ya bayyana cewa ƙasarsa za ta amince da kafa ƙasar Falasdinu a wani taron Majalisar Ɗinkin Duniya da za a gudanar a watan Satumba, muddin Isra’ila ba ta ɗauki matakin kawo ƙarshen rikicin Gaza da kuma amincewa da tsagaita wuta ba.

A makon da ya gabata, Shugaban Ƙasar Faransa, Emmanuel Macron, ya tabbatar da cewa Faransa za ta amince da kafa ƙasar Falasdinu a hukumance yayin zaman Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 da za a yi a watan Satumba.

(Xinhua/NAN)