Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da tsawaita wa’adin shugaban hukumar kwastam ta ƙasa, Mista Bashir Adewale Adeniyi, da shekara guda, wanda wa’adinsa na farko ya kamata ya ƙare a ranar 31 ga Agusta, 2025.
A cewar wata sanarwa daga Fadar Shugaban Ƙasa da mai ba Shugaban Ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya sanya wa hannu, an bayyana cewa wannan tsawaitawa na nufin bai wa Adeniyi damar kammala muhimman sauye-sauyen da ake aiwatarwa a hukumar kwastam da kuma manyan ayyukan da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa.
Daga cikin muhimman ayyukan da tsawaitawar ke da nufin cika akwai: sauya fasalin hukumar kwastam da zamani, aiwatar da shirin National Single Window Project, da kuma cika alkawuran da Najeriya ta ɗauka ƙarƙashin tsarin yarjejeniyar African Continental Free Trade Area (AfCFTA).
Shugaba Tinubu ya yabawa Mista Adeniyi bisa “jajircewarsa da nagartaccen shugabancinsa,” tare da bayyana kwarin guiwar cewa wannan tsawaitawa za ta ƙarfafa rawar da hukumar kwastam ke takawa wajen sauƙaƙa harkokin kasuwanci, samar da kuɗaɗen shiga ga ƙasa, da tabbatar da tsaron iyakoki.
Sanarwar ta fito ne daga Fadar Shugaban Ƙasa dake Abuja a ranar Laraba, 31 ga Yuli, 2025.
