Trends

Bangaren Kere-Kere Ya Farfado, Ya Ba Da Kaso 9.57% Ga GDP — NBS

National Bureau of Statistics (NBS) ta bayyana cewa bangaren masana’antu (manufacturing) ya ba da gudummawar kashi 9.57 cikin dari ga hakikanin GDP a rubu’in farko na shekarar 2026, lamarin da ke nuna farfadowar bangaren daga kashi 7.40 cikin dari da aka samu a rubu’in karshe na 2025.

Duk da cewa wannan kaso ya dan yi kasa kadan idan aka kwatanta da kashi 9.62 cikin dari da aka samu a rubu’in farko na 2025, bangaren ya nuna karfin bunkasa mai kyau a shekarar nan.

Rahoton ya nuna cewa bangaren ya samu ci gaban GDP na kashi 3.29 cikin dari a shekara-shekara, wanda ya dara rubu’in da ya gabata da kuma makamancin lokacin bara.

Haka kuma, ci gaban daga rubu’i zuwa rubu’i ya kai kashi 3.59 cikin dari, yayin da ci gaban GDP na kudi (nominal GDP) ya karu da kashi 10.22 cikin dari idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

Bangaren ya kuma bayar da kashi 10.08 cikin dari na GDP na kudi, wanda ya ragu daga kashi 10.78 cikin dari a rubu’in farko na 2025, amma ya fi kashi 8.34 cikin dari na rubu’in karshe na 2025.

NBS ta ce: “Ci gaban hakikanin GDP a bangaren masana’antu a rubu’in farko na 2026 ya kai kashi 3.29 cikin dari, wanda ya fi na makamancin lokacin 2025 kuma ya fi rubu’in da ya gabata da maki 1.60 da 2.17 bi da bi.”

Farfadowar bangaren ta samo asali ne daga karuwar ayyuka a bangarorin kayayyakin amfani, siminti, sarrafa abinci, kayan masana’antu da kuma gine-gine.

Har ila yau, harajin VAT ya nuna muhimmancin bangaren, inda masana’antu suka samar da Naira tiriliyan 1.17 a shekarar 2025, daga Naira biliyan 803.53 a 2024.

Duk da wannan ci gaba, masana’antun na ci gaba da fuskantar kalubale kamar tsadar wutar lantarki, matsalolin sufuri, rashin tsaro, rashin daidaiton canjin kudi, yawan haraji da kuma karin kudin sarrafa kayayyaki.

A bangaren gaba daya kuwa, tattalin arzikin Najeriya ya karu da kashi 3.89 cikin dari a rubu’in farko na 2026, yayin da jimillar GDP ta kai Naira tiriliyan 110.79, daga Naira tiriliyan 94.05 a makamancin lokacin 2025.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *