Trends

Najeriya Ta Shigo Da Sinadarin Zakin Rogo na Naira Biliyan 8 — Rahoto

Najeriya ta shigo da kimanin tan 7,700 na sinadarin sorbitol da darajarsa ta kai Naira biliyan 8 (dala miliyan 6.1) a shekarar 2023, abin da ke nuna yadda kasar ke dogaro da sinadaran zaki na masana’antu daga waje, a cewar wani sabon rahoto.

Rahoton, wanda Nigeria Cassava Investment Accelerator (NCIA) ta fitar mai taken NCIA Insights: Unlocking Cassava’s Industrial Value through Sorbitol Production, ya nuna cewa bukatar sinadaran zaki a Najeriya za ta kai tan miliyan 2.15 a shekarar 2026, yayin da karfin samar da cikin gida ke tsaya a tan 53,000 kacal — wanda ke rufe kashi 2.5 cikin dari na bukata.

Sorbitol, wanda ake amfani da shi sosai a magunguna, kayayyakin kula da baki, kayan zaki da sarrafa abinci, ana yawan samar da shi daga masara. Sai dai NCIA ta bayyana cewa cassava na da yawan starch da ke ba shi damar zama madadin samar da sinadarin.

Rahoton ya ce: “A matsayinta na kasa mafi yawan noman cassava a duniya, Najeriya na da babbar dama ta samar da sorbitol a cikin gida tare da biyan bukatu a masana’antu daban-daban.”

An bayyana kamfanin Psaltry International Company Limited a matsayin daya daga cikin kamfanonin da ke kokarin rage gibin samar da sinadarin. A shekarar 2022, kamfanin ya kaddamar da masana’antar farko ta sorbitol da aka samar daga cassava a Iseyin, Jihar Oyo, wadda ke da karfin samar da tan 25 a kowace rana.

NCIA ta kuma bayyana matakan samar da sorbitol, daga shigar da cassava, fitar da starch, canza shi zuwa glucose syrup ta hanyar enzymes, sannan a mayar da shi sorbitol ta hanyar hydrogenation. Ta ce ingancin dawo da starch yana da matukar muhimmanci wajen samun riba da yawan amfanin gona.

Rahoton ya jaddada cewa sorbitol na da amfani sosai a masana’antu kamar man goge baki, wanke baki, chewing gum da magunguna, inda ya bukaci karin zuba jari a bangaren cassava domin rage dogaro da shigo da kaya daga waje.

Masana tattalin arziki sun ce idan aka fadada samar da sorbitol a cikin gida, hakan na iya karfafa masana’antar magunguna da abinci, rage fitar da kudin waje, tare da mayar da Najeriya cibiyar samar da sinadaran zaki a yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *