Gwamnatin Najeriya ta soke jimillar dala miliyan 717.7 da ba a fitar ba daga tallafin Bankin Duniya da aka ware domin shirin Power Sector Recovery Performance-Based Operation (PSRO), wanda aka tsara don dawo da daidaito da dorewar bangaren wutar lantarki.
A cewar takardar sake tsari da aka samu daga Nairametrics, gwamnatin tarayya ta aika bukatar soke kudin a ranar 26 ga Maris, 2026, kuma World Bank ta amince ta karkatar da tallafin zuwa wasu hanyoyin taimako. Haka kuma an matsar da ranar kammala shirin daga Yuni 2027 zuwa Mayu 2026.
Bankin Duniya ya ce babban dalilin rugujewar shirin shi ne faduwar darajar Naira da kuma rashin daidaita farashin wutar lantarki, lamarin da ya kara gibin kudin da bangaren ke fuskanta.
Rahoton ya nuna cewa gibin kudin tallafin wutar lantarki ya karu daga Naira biliyan 140 a 2022 zuwa Naira tiriliyan 1.9 a 2024 da 2025, abin da ya hana cimma manufofin gyare-gyare.
Duk da tashin farashin gas da ake amfani da shi wajen samar da wuta — wanda ake saye da dalar Amurka — farashin wutar lantarki bai canza ga yawancin masu amfani ba, sai dai masu amfani a rukunin Band A da aka yi musu gyara a Afrilu 2024. Wannan rashin daidaito ya haifar da babban gibi na kudi.
Rahoton ya kuma nuna matsaloli kamar raunin rarraba wuta, tangardar watsawa (transmission bottlenecks), rashin amfani da cikakken karfin samar da wuta, da kuma asarar wuta a fasaha da kasuwanci, wadanda ke rage damar dawo da kudin aiki.
Shirin PSRO, wanda aka amince da shi a shekarar 2020, ya fara kawo ci gaba inda gibin kudin wuta ya ragu da kashi 71 cikin dari tsakanin 2019 zuwa 2022, sannan ingancin dawo da kudin da dokoki suka tanada ya karu daga kashi 56 zuwa 94 cikin dari.
Bankin Duniya ya amince da karin tallafi na dala miliyan 750 a 2023, amma an fitar da kashi 9 kacal saboda jinkirin aiwatar da gyare-gyare.
Takardar sake tsari ta nuna cewa jimillar kudin da aka amince da shi ya kai dala biliyan 1.51, inda aka riga aka fitar da dala miliyan 796 kafin soke ragowar dala miliyan 717.7 da ba a fitar ba.
Akanta-Janar na Tarayya, Dakta Shamseldeen Ogunjimi, ya taba gargadi cewa jinkirin amincewa da fitar da lamuni na iya sa Najeriya ta janye daga shirye-shiryen Bankin Duniya, yana mai cewa: “Kudin da ake nema lamuni ne, ba tallafi ba, kuma Najeriya na da hakkin a duba bukatunta cikin lokaci.”
