Trends

Afirka Ta Tattara Dala Miliyan 498.8 Don Yaki Da Barkewar Ebola

Cynthia Goldsmith This colorized transmission electron micrograph (TEM) revealed some of the ultrastructural morphology displayed by an Ebola virus virion. See PHIL 1181 for a black and white version of this image. What is Ebola hemorrhagic fever (Ebola HF)?

Ebola hemorrhagic fever (Ebola HF) is a severe, often-fatal disease in humans and nonhuman primates (monkeys, gorillas, and chimpanzees) that has appeared sporadically since its initial recognition in 1976.

The disease is caused by infection with Ebola virus, named after a river in the Democratic Republic of the Congo (formerly Zaire) in Africa, where it was first recognized. The virus is one of two members of a family of RNA viruses called the Filoviridae. There are four identified subtypes of Ebola virus. Three of the four have caused disease in humans: Ebola-Zaire, Ebola-Sudan, and Ebola-Ivory Coast. The fourth, Ebola-Reston, has caused disease in nonhuman primates, but not in humans.

Afirka ta samu kimanin dala miliyan 498.8 a matsayin alkawuran tallafi domin karfafa matakan dakile barkewar cutar Ebola nau’in Bundibugyo da ke ci gaba da yaduwa, wadda ta riga ta yi sanadin mutuwar mutane 220.

Shugaban Hukumar CDC ta Afirka, Africa Centres for Disease Control and Prevention, Jean Kaseya ne ya bayyana hakan a wani babban taron ministoci kan lafiya.

Ya ce: “Gwamnatoci da abokan hulda sun sanar da kimanin dala miliyan 498.8 a matsayin alkawuran tallafi domin karfafa matakan yaki da cutar a kasashen da abin ya shafa da kuma wadanda ke cikin hadarin kamuwa.”

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, World Health Organization, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya tabbatar da karuwar yawan wadanda suka mutu, inda ya yi gargadi cewa: “A halin yanzu, cutar na gabanmu a yawan yaduwa.”

Barkewar cutar ta shafi Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo (DRC) da Uganda. A DRC, hukumomi sun ce akwai mutane 906 da ake zargi, 105 da aka tabbatar sun kamu, 223 wadanda ake zargin sun mutu, da kuma 10 da aka tabbatar sun mutu.

A Uganda kuwa, an tabbatar da kamuwa da mutane bakwai, yayin da mutum daya ya mutu, mafi yawansu suna da alaka da farkon yaduwar cutar.

Nau’in Bundibugyo da ke haddasa wannan barkewar cuta ba kasafai ake samunsa ba, kuma har yanzu babu allurar rigakafi ko magani na musamman da aka amince da shi.

Yawancin alluran rigakafin da ake da su an kera su ne domin nau’in Zaire, wanda ya haddasa annobar Yammacin Afirka ta 2014 zuwa 2016 da ta kashe fiye da mutane 11,000.

Abokan hulda na kasa da kasa sun shiga cikin shirin yaki da cutar, inda Bankin Duniya ya yi alkawarin dala miliyan 160 ga Kongo, Amurka ta bayar da dala miliyan 82, yayin da kasashen Turai suka yi alkawarin dala miliyan 57. Haka kuma hukumar agajin Majalisar Dinkin Duniya ta ware dala miliyan 60 daga asusun gaggawa.

Kaseya ya jaddada cewa amincewa, hadin kai da gaggauta daukar mataki suna da matukar muhimmanci wajen dakile yaduwar cutar, yana mai cewa wannan tallafi ya nuna hadin kan Afirka da kuma nauyin da ke kan kowa na kare lafiyar jama’a.

Masana sun yi gargadin cewa idan ba a dauki matakan gaggawa ba, cutar na iya kara bazuwa, musamman ganin rashin allurar rigakafi, yanayin wuraren da cutar ke yaduwa, da kuma saurin yaduwar ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *