National Bureau of Statistics (NBS) ta bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya ya bunkasa da kashi 3.89 cikin dari a rubu’in farko na shekarar 2026, inda bangarorin noma, sadarwa, ayyukan kudi, gine-gine da kasuwanci suka jagoranci ci gaban.
Rahoton ya nuna cewa wannan ci gaban ya dara kashi 3.13 cikin dari da aka samu a rubu’in farko na shekarar 2025, lamarin da ke nuna irin gagarumar gudunmawar bangaren da ba na mai ba, wanda ya bayar da kaso 96.08 cikin dari na hakikanin GDP.
NBS ta ce, “Jimillar Kayayyakin Cikin Gida (GDP) ta karu da kashi 3.89 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara, wanda ya fi kashi 3.13 cikin dari da aka samu a rubu’in farko na 2025.”
Bangaren noma ya samu ci gaba da kashi 3.15 cikin dari idan aka kwatanta da kashi 0.07 cikin dari a shekarar 2025, yayin da bangaren masana’antu ya bunkasa da kashi 3.50 cikin dari.
Bangaren ayyuka kuwa ya karu da kashi 4.31 cikin dari, inda ya bayar da kaso 57.73 cikin dari na GDP, abin da ya sanya shi zama mafi girman bangare a tattalin arzikin kasar.
Hakazalika, GDP a kimar kudi ya karu zuwa Naira tiriliyan 110.79 daga Naira tiriliyan 94.05 a rubu’in farko na shekarar 2025, wanda ke nuna karin kashi 17.79 cikin dari idan aka kwatanta da bara.
Rahoton ya nuna cewa yawan danyen man fetur da Najeriya ke hakowa ya ragu zuwa ganga miliyan 1.55 a rana daga ganga miliyan 1.62 a makamancin lokacin bara, sai dai duk da haka bangaren mai ya samu ci gaba da kashi 2.57 cikin dari, inda ya bayar da kaso 3.92 cikin dari na GDP.
Daga cikin bangarorin da ba na mai ba da suka jagoranci habakar tattalin arzikin akwai bangaren sadarwa da ya bunkasa da kashi 10.98 cikin dari tare da bayar da kaso 11.31 cikin dari na GDP, bangaren hada-hadar kudi da inshora da ya samu ci gaba da kashi 8.54 cikin dari tare da kaso 3.76 cikin dari, bangaren gine-gine da ya karu da kashi 6.38 cikin dari tare da kaso 4.85 cikin dari, da kuma bangaren kere-kere wanda ya bunkasa da kashi 3.29 cikin dari tare da kaso 9.57 cikin dari.
Kasuwanci ne ya kasance mafi girman bangare, inda ya bayar da kaso 17.89 cikin dari na GDP.
Sauran bangarorin da suka samu karfi sun hada da nishadi da wasanni da suka bunkasa da kashi 11.25 cikin dari, samar da ruwa da kula da sharar gida da suka karu da kashi 10.32 cikin dari, da kuma sufuri da ajiya da suka bunkasa da kashi 7.41 cikin dari.
Sai dai bangaren wutar lantarki da iskar gas ya samu koma baya da kashi 15.30 cikin dari.
A wani bangare kuma, World Bank ta rage hasashen ci gaban tattalin arzikin Najeriya zuwa kashi 4.1 cikin dari na shekarar 2026, tana mai danganta hakan da rashin tabbas a tattalin arzikin duniya da sauyin farashin mai.
