Trends

Amintar Masu Zuba Jari Ta Kara Wa NGX Darajar Naira Biliyan 906

Kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya, Nigerian Exchange Group (NGX), ta fara makon nan da gagarumin ci gaba bayan da amincewar masu zuba jari ta kara darajar kasuwar da kashi 0.57 cikin dari, sakamakon karin farashin hannayen jarin Airtel Africa Plc da wasu kamfanoni 34.

All-Share Index ya karu da maki 1,412.65 inda ya rufe a kan maki 251,125.02, yayin da jimillar darajar kasuwar ta karu da Naira biliyan 906 zuwa Naira tiriliyan 160.983.

Hakan ya sa ribar watan zuwa yanzu ta kai kashi 3.7 cikin dari, yayin da ribar shekarar zuwa yanzu ta kai kashi 61.4 cikin dari, abin da ke nuna ci gaba mai dorewa a kasuwar.

Kamfanin Cowry Assets Management Limited ya bayyana cewa ana sa ran wannan yanayin ci gaba zai dore, sakamakon sabuwar kwarin gwiwar masu zuba jari da kuma sauye-sauyen da suke yi a tsarin jarinsu.

Rahoton ya nuna cewa kamfanoni 35 sun samu karin darajar hannayen jari, yayin da kamfanoni 30 suka yi asara.

Airtel Africa Plc ce ta jagoranci masu samun riba bayan da farashin hannun jarinta ya karu da kashi 10 cikin dari zuwa Naira 3,655.70 kowanne.

Sauran kamfanonin da suka samu karin farashi sun hada da International Energy Insurance da kashi 9.68 cikin dari, Sovereign Trust Insurance da kashi 9.65 cikin dari, Caverton Offshore da kashi 9.63 cikin dari, da kuma VFD Group da kashi 9.55 cikin dari.

A bangaren masu asara kuwa, McNichols Plc ta yi asarar kashi 10 cikin dari inda ta rufe a kan Naira 7.20 kowanne, sai The Initiates Plc da kashi 9.91 cikin dari, Learn Africa Plc da kashi 9.69 cikin dari, Zichis Agro Allied da kashi 7.93 cikin dari, da May & Baker Nigeria Plc da kashi 6.60 cikin dari.

Sai dai kuma yawan hada-hadar kasuwa ya ragu, inda jimillar cinikayya ta sauka da kashi 30.2 cikin dari zuwa hannayen jari miliyan 497.09 da aka yi mu’amalarsu kan Naira biliyan 31.62 ta cikin hada-hada 74,129.

Access Holdings Plc ce ta fi kowanne yawan cinikayya da hannayen jari miliyan 61.29 da darajarsu ta kai Naira biliyan 1.53, sai Zenith Bank Plc da hannayen jari miliyan 37.93 da suka kai Naira biliyan 4.99, Fidelity Bank Plc da hannayen jari miliyan 35.80 da suka kai Naira miliyan 851, Japaul Gold da hannayen jari miliyan 24.67 da suka kai Naira miliyan 90.9, sai Tantalizers Plc da hannayen jari miliyan 22.79 da suka kai Naira miliyan 103.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *