Trends

Mallakar Matatun Mai: NNPC Ta Kulla Yarjejeniya da Kamfanonin China

Kamfanin Man Fetur na Kasa, Nigerian National Petroleum Company Limited, na duba yiwuwar tsarin hadin gwiwar mallaka irin na NLNG wanda zai iya bai wa masu zuba jari daga kasar China kaso mafi rinjaye na kusan kashi 51 cikin 100 a matatun mai na Port Harcourt da Warri, a wani bangare na shirin farfado da matatun da kuma mayar da su cibiyoyin kasuwanci masu dorewa.

Bayanan sun fito ne bayan da NNPC ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da kamfanonin China biyu, Sanjiang Chemical Company Limited da Xinganchen (Fuzhou) Industrial Park Operation and Management Co. Ltd..

An sanya hannu kan yarjejeniyar ne a birnin Jiaxing a ranar 30 ga Afrilu, 2026, tsakanin Shugaban Kamfanin NNPC, Bayo Ojulari, da shugabannin kamfanonin biyu na China. Yarjejeniyar ta kunshi yiwuwar hadin gwiwar fasaha da mallaka.

Majiyoyi sun shaida wa jaridar The Punch cewa tsarin da ake shirin aiwatarwa ya wuce kwangilar gyaran matatun mai kawai, domin yana iya hada da mallakar hannun jari na dogon lokaci, gudanarwa tare, da shiga harkokin aiki kamar yadda ake yi a tsarin Nigeria LNG Limited.

A karkashin hadin gwiwar, kamfanonin China za su taimaka wajen kammala ayyukan da suka rage a matatun, samar da ayyukan gudanarwa da kula da su, tare da kara karfinsu domin dacewa da ka’idojin samar da mai mai tsafta.

Ojulari ya bayyana yarjejeniyar a matsayin babban ci gaba bayan watanni shida na tattaunawa.

Ya ce, “Dukkan bangarorin sun fahimci akwai damar hadin gwiwa mai anfani wajen bunkasa kadarorin tace mai na NNPC a Najeriya da kuma tabbatar da ribar da za ta dore na dogon lokaci.”

Yarjejeniyar ta kuma hada da yiwuwar fadada ayyuka zuwa bangaren sinadarai na petrochemical da masana’antun da suka danganci iskar gas ta hanyar samar da cibiyoyi kusa da matatun man.

Masana sun ce tsarin mallakar hannun jarin na nuna damuwar NNPC kan dorewar tsare-tsaren gyaran matatun da aka yi a baya.

Sakataren zartarwa na kungiyar Major Energies Marketers Association of Nigeria, Clement Isong, ya yaba da matakin.

Ya ce, “Wannan wata sabuwar hanya ce ta tabbatar da kadarorin suna aiki yadda ya kamata kuma cikin dorewa. Bambancin shi ne cewa bangare na uku zai mallaki kaso a matsayin abokin huldar kasuwanci, don haka zai yi kokarin ganin matatar tana aiki domin samun riba daga jarinsa.”

Sai dai yarjejeniyar ba ta zama doka kai tsaye ba tukuna, domin aiwatar da ita zai dogara ne kan cikakken bincike na fasaha, kuɗi, kasuwanci da doka, tare da samun amincewar hukumomin da suka dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *