Kananan da matsakaitan masana’antu (SMEs) a Najeriya sun taimaka wajen kara wa tattalin arzikin kasar dala biliyan 2 ta hanyar tallace-tallace da aka gudanar a kafafen sada zumunta, kamar yadda wani sabon rahoto daga kamfanin bincike mai zaman kansa na Public First ya bayyana.
Rahoton ya nuna cewa kananan da matsakaitan sana’o’i miliyan 14 a Najeriya sun yi amfani da dandamalin Meta Platforms — da suka hada da Facebook, Instagram, WhatsApp, Messenger, Meta AI da Threads — wajen farawa da bunkasa kasuwancinsu a bara.
Rahoton ya ce hakan ya samar da karin inganci a harkokin kasuwanci da ya kai kimanin dala miliyan 640 ta hanyar amfani da sakonnin gaggawa wajen sadarwa.
SMEs na da kaso sama da kashi 96 cikin 100 na dukkan kasuwancin Najeriya, kuma suna daukar kusan kashi 84 cikin 100 na ma’aikatan kasar tare da bayar da gudunmawa fiye da kashi 45 cikin 100 ga GDPn kasa.
Duk da kalubale irin su tsadar rance, rashin ingantattun ababen more rayuwa, da yawan haraji, SMEs na ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen samar da ayyukan yi da kirkire-kirkire a fannoni kamar cinikayya, noma da masana’antu.
Dandamalin Meta sun zama muhimman hanyoyin talla da gano kwastomomi ga kasuwancin Najeriya. Rahoton ya nuna cewa kashi 81 cikin 100 na kasuwancin intanet da aka gudanar da bincike a kansu sun ce Facebook, Instagram da WhatsApp sun taimaka wajen fadada yawan kwastomominsu fiye da yankunansu.
Darakta a Public First, Alison Neyle, ta ce sauyin fasahar dijital a Najeriya na samar da sababbin damammaki ga ‘yan kasuwa, masu kirkire-kirkire da masu amfani da kayayyaki.
Ta ce, “Dandamalin Meta na taimaka wa kamfanonin Najeriya wajen bunkasa kasuwanci a bangarori na hukuma da wadanda ba na hukuma ba, tare da karfafa harkokin kasuwanci da shiga cikin daya daga cikin tattalin arzikin dijital mafi saurin bunkasa a duniya.”
Rahoton mai taken “Nigeria’s Digital Economy” ya kuma bayyana irin damar da fasahar basirar wucin gadi (AI) ke da ita. Ya yi hasashen cewa AI zai iya kara wa GDPn Najeriya dala biliyan 22 nan da shekarar 2035, inda WhatsApp zai kasance babbar hanyar amfani da AI ga ‘yan Najeriya.
Rahoton ya ce kashi 93 cikin 100 na tambayoyin da ake yi wa Meta AI a yankin Saharar Afirka ana yin su ne ta WhatsApp, lamarin da ke nuna yadda amfani da AI ke yaduwa ta hanyoyin sadarwar yau da kullum.
Daraktar manufofin jama’a ta Meta a yankin Saharar Afirka, Balkissa Ide Siddo, ta ce Najeriya na daya daga cikin kasuwannin duniya mafi kuzari da kirkire-kirkire da amfani da fasahar dijital.
Ta ce, “Daga mai dinki a Lagos da ke samun kwastomomi ta Instagram, zuwa dan kasuwa a Kano da ke karbar oda ta WhatsApp, dandamalin Meta na cire tsoffin shingaye ga ci gaban kasuwanci tare da bude sabbin damammakin tattalin arziki.”
Rahoton ya karkare da cewa idan aka ci gaba da zuba jari a bangaren sadarwa, samar da manufofi masu kyau, da bunkasa AI mai dacewa da ‘yan Afirka, Najeriya na da damar jagorantar sabon zamani na bunkasar tattalin arzikin dijital a nahiyar Afirka.
