Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana cewa barkewar cutar Ebola da ake fama da ita a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo (DRC) na da matukar hadari a cikin kasar da yankin da ke kewaye da ita, amma hadarin bai kai matakin duniya baki daya ba.
Babban Daraktan WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce bincike ya nuna cewa barkewar cutar a gabashin DRC mai yiwuwa ta fara ne tun watanni biyu da suka gabata, yayin da adadin wadanda aka tabbatar sun kamu ya kai 51 a lardunan Ituri da North Kivu.
Ya kara da cewa, “Ko da yake mun san girman barkewar cutar a DRC ya fi haka yawa.”
Kasar Uganda ma ta tabbatar da kamuwa da mutum biyu da cutar a Kampala, ciki har da mutum daya da ya mutu, yayin da wani dan kasar Amurka da ke aiki a DRC ya kamu da cutar kafin a kai shi Jamus domin kula da lafiyarsa.
Tedros ya yi gargadin cewa baya ga wadanda aka tabbatar sun kamu, akwai kusan mutane 600 da ake zargin sun kamu da cutar da kuma mutuwar mutane 139 da ake zargi na da alaka da Ebola.
Ya ce ana sa ran alkaluman za su ci gaba da karuwa saboda cutar ta dade tana yaduwa kafin a gano ta.
A ranar Lahadi, WHO ta ayyana lamarin a matsayin Public Health Emergency of International Concern (PHEIC), wato gaggawar lafiya ta duniya, wanda shi ne mataki na biyu mafi girma a dokokin lafiya na kasa da kasa.
Sai dai kwamitin gaggawa na WHO ya bayyana cewa barkewar cutar ba ta kai matsayin annobar duniya gaba daya ba.
Shugabar kwamitin, Lucille Blumberg, ta ce halin da ake ciki ya cika sharuddan ayyana gaggawar lafiya ta duniya, amma bai kai matsayin annobar duniya ba.
Jami’ar fasaha ta WHO, Anais Legand, ta bayyana cewa manyan matakan da ake dauka yanzu sun hada da bibiyar wadanda suka yi hulda da masu cutar, killace wadanda ake zargi da kamuwa, da kuma kula da marasa lafiya domin dakile yaduwar cutar.
A gefe guda kuma, Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya soki yadda WHO ta dauki lokaci kafin mayar da martani, yana mai cewa hukumar ta yi “dan jinkiri.”
Sai dai Tedros ya kare WHO, yana mai cewa watakila kalaman Rubio sun samo asali ne daga rashin fahimtar yadda dokokin lafiya na kasa da kasa ke aiki, domin WHO tana tallafawa kasashe ne wajen yaki da barkewar cututtuka ba wai maye gurbinsu ba.

