Hukumar Tara Haraji ta Kasa (NRS) ta sanya burin tattara harajin da ya kai naira tiriliyan 40 a shekarar 2026, tare da jaddada muhimmancin hadin gwiwa da gwamnatocin jihohi domin cimma wannan buri.
Shugaban Hukumar NRS, Zacch Adedeji, wanda Mohammed Lawal ya wakilta, ne ya bayyana hakan yayin wani taron kasa da aka gudanar a Abuja kan karfafa bin dokokin haraji karkashin sabon tsarin.
Ya ce cimma burin naira tiriliyan 40 zai bukaci karin horas da ma’aikata, bunkasa gaskiya da rikon amana, da kuma hadin gwiwa mai karfi tsakanin hukumomin tarayya, jihohi da kananan hukumomi domin magance matsalolin da ke hana bin dokokin haraji yadda ya kamata.
Adedeji ya kuma bayyana cewa hukumar na shirin karrama jihohin da suka fi bin ka’idojin biyan haraji a karshen shekarar 2026 domin karfafa gwiwar gwamnatocin jihohi wajen inganta bin dokokin haraji.
Taron ya mayar da hankali ne kan wayar da kan jama’a da masu ruwa da tsaki game da wajibcin cire haraji da mika kudaden da aka tara, tare da ilmantar da su kan tanade-tanaden sabbin dokokin haraji domin rage kalubalen sauyin tsarin.
Ministan Kudi, Taiwo Oyedele, wanda Tolu Adegbie ya wakilta, ya ce sabon tsarin harajin na daga cikin manyan sauye-sauyen tattalin arziki da suka hada da sassauta darajar naira, cire tallafin mai da kokarin dakile hauhawar farashi.
Ya bayyana cewa an tsara sauye-sauyen ne domin samar da daidaito da dorewar hanyoyin samun kudaden shiga na gwamnati domin tallafa wa gine-ginen more rayuwa, lafiya, ilimi da tsaro.
Oyedele ya tabbatar da cewa sauye-sauyen ba za su kara wa ‘yan kasa nauyin haraji ba, sai dai za su fadada yawan masu biyan haraji, yana mai cewa amfani da fasaha zai taimaka wajen toshe hanyoyin karkatar da kudaden shiga tare da kara yawan masu biyan haraji da son ransu a fadin kasar.
Ya kuma jaddada cewa tsarin rabon iko da kudaden gwamnati tsakanin matakan gwamnati zai samu nasara ne kawai idan akwai hadin kai, daidaitattun tsare-tsare da kuma gaskiya tsakanin gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi.
Hukumar NRS ta sake jaddada aniyarta ta hada kai wajen tsara harkokin haraji a fadin kasar, tabbatar da gaggawar mika kudaden harajin da aka cire, da kuma gina tsari mai gaskiya da inganci domin biyan bukatun kudaden shiga na Najeriya.

