Trends

FG Za Ta Fara Karɓar Harajin VAT Kashi 7.5 Chajin Kuɗi Ta Wayar Salula da USSD

Gwamnatin Tarayya ta sanar da fara aiwatar da harajin ƙarin daraja (VAT) kashi 7.5 cikin 100 kan wasu ayyukan banki na lantarki, domin ƙarfafa bin dokokin biyan haraji, faɗaɗa hanyoyin samun kuɗaɗen shiga da kuma daidaita tattalin arziƙin dijital na Najeriya da dokokin haraji da ake da su.

Harajin VAT ɗin, wanda zai fara aiki daga ranar Litinin, 19 ga Janairu, 2026, zai shafi kuɗin hidima da ake caji kan canja kuɗi ta banki ta wayar salula, mu’amalar USSD da sauran ayyukan banki na lantarki da doka ta amince da su.

Bisa ga umarnin hukumomin haraji, yanzu an wajabta wa bankuna da cibiyoyin kuɗi na fasahar zamani (fintechs) su riƙa karɓa tare da tura harajin VAT kan kuɗin hidimar mu’amalar lantarki da abin ya shafa zuwa Hukumar Tara Haraji ta Najeriya (NRS), wadda a baya ake kira Hukumar Tara Haraji ta Tarayya (FIRS).

Manufar na daga cikin manyan shirye-shiryen sauya fasalin kuɗaɗen gwamnati na Tarayya, da nufin ƙara samun kuɗaɗen shiga ba daga man fetur ba, tare da tabbatar da cewa ayyukan kuɗi na dijital da ke ƙaruwa cikin sauri suna ba da gudummawa yadda ya kamata ga kuɗaɗen shiga na ƙasa.

Tuni wasu bankuna da kamfanonin fintech suka fara sanar da kwastomominsu game da wannan sauyi. A wata sanarwa da kamfanin Moniepoint ya aikewa masu amfani da shi, ya bayyana cewa cire VAT ba sabon caji ba ne daga bankuna, illa dai wajibi ne na doka da gwamnati ta tanada.
“Daga ranar Litinin, 19 ga Janairu, 2026, an wajabta mana karɓar VAT kashi 7.5 cikin 100, wanda za a tura zuwa Hukumar Tara Haraji ta Najeriya,” in ji sanarwar.

Jami’ai sun fayyace cewa za a riƙa karɓar VAT ne kawai kan kuɗin hidima da bankuna da fintechs ke caji, kamar kuɗin canja kuɗi ko amfani da USSD, ba kan ainihin kuɗin da ake turawa ko ajiyar kuɗin kwastoma ba.

Masana sun ce wannan mataki na nuna ƙoƙarin gwamnati na toshe ɓarnar kuɗaɗen shiga, ƙara gaskiya a tsarin kuɗi da kuma shigar da ayyukan banki na lantarki gaba ɗaya cikin tsarin biyan haraji na ƙasa, musamman ganin yadda mu’amalar dijital ke ƙaruwa a faɗin Najeriya.

An shawarci jama’a da su lura da ranar fara aiwatar da dokar, tare da la’akari da harajin VAT a cikin shirye-shiryensu na amfani da ayyukan banki na lantarki nan gaba.