Trends

Likitoci Na Bukatar Ci Gaba da Karin Horaswa a Fannin Kiwon Lafiya – Lauya

Kiwon lafiya Kiwon lafiya

Wani lauya, Dayo Adu, ya ce likitoci na bukatar ci gaba da samun horo a fannin doka da kiwon lafiya (medical-legal training) domin su fahimci nauyin aikinsu da kuma haƙƙin marasa lafiya yadda ya kamata.

Adu ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin The Morning Brief na gidan talabijin na Channels Television a ranar Laraba, inda ya jaddada muhimmancin wayar da kan likitoci kan al’amuran doka da al’adu da suka shafi aikinsu.
A cewarsa, akwai gibi a fannin horon doka ga likitoci, har ma a cikin shirye-shiryen ci gaba da ilimi da ake yi wa likitoci.

“Na kuma yi imanin cewa akwai gibi idan ana maganar horon doka a fannin kiwon lafiya, ko da a cikin ci gaba da ilimin likitoci. Wataƙila haɗin gwiwa da lauyoyi ko ƙungiyoyin shari’a zai taimaka wa likitoci su fi sanin nauyin da ke kansu,” in ji shi.

Da yake magana kan haƙƙin marasa lafiya, Adu ya bayyana cewa ya zama dole a wayar da marasa lafiya kan irin kulawar da ya dace su samu daga likitoci.

“Ga marasa lafiya, abu ne na fahimtar haƙƙinsu da sanin cewa irin kulawar da suka cancanta haƙƙinsu ne, kuma dole ne a bi ka’idojin kulawa yadda ya kamata,” ya ƙara da cewa.

Ya kuma jaddada muhimmancin wayar da kan jama’a, yana mai cewa marasa lafiya na bukatar cikakken bayani domin su iya neman gaskiya da ɗaukar mataki idan an yi kuskure.

Lauyan ya kuma shawarci masu aikin likitanci da su duba kansu, tare da amincewa da matsalolin tsarin da ke akwai a fannin kiwon lafiya.

“Ina ganin ya kamata aikin likitanci da kansa ya duba ciki. Mun san cewa kudade ba su wadatar, ma’aikata a asibitoci ba su kai yadda ya kamata ba, kuma dukkanmu mun san batun ‘japa’,” in ji shi.

Sai dai Adu ya lura cewa a wasu lokuta, wasu ƙwararrun likitocin Najeriya da ke ƙasashen waje suna fara dawowa gida domin kafa cibiyoyin kiwon lafiya na musamman da za su biya bukatun marasa lafiya.

Duk da haka, ya jaddada cewa har yanzu akwai sauran aiki mai yawa da ya kamata a yi, musamman wajen tabbatar da cewa asibitoci suna bin ƙa’idojin da hukumomin kula da kiwon lafiya suka gindaya.

Jawaban nasa sun biyo bayan rasuwar wani yaro dan watanni 21, wanda aka ruwaito cewa ɗan shahararriyar marubuciyar Najeriya, Chimamanda Ngozi Adichie, ne, wanda ya rasu a ranar 7 ga Janairu a Asibitin Euracare. An yi zargin cewa sakaci daga likitan sa barci (anaesthesiologist) ne ya haddasa mutuwar.

Marubuciyar ta riga ta miƙa wa asibitin takardar gargadi ta shari’a, tana zargin cewa sakacin likitoci da rashin bin ƙa’idojin aiki ne suka jawo mutuwar ɗanta.