Super Eagles ta Najeriya ta sha kashi da ci 4-2 a bugun fenareti a hannun Morocco a wasan kusa da na ƙarshe na gasar Kofin Ƙasashen Afirka na 2025 (AFCON), wanda aka buga a daren Laraba.
Najeriya ta kasa ƙirƙirar isassun damar zura ƙwallo a raga, tare da rashin cin gajiyar kaɗan daga cikin damar da suka samu a wasan.
Bayan kammala mintuna 90 na wasan, babu wata ƙungiya da ta samu damar zura ƙwallo, yayin da duka bangarorin biyu suka yi ta fama wajen samun nasarar kai hari.
Haka nan ma bayan ƙarin mintuna 30 (jimillar mintuna 120), wasan ya ci gaba da karewa babu ci babu cinyewa, lamarin da ya sa aka yanke hukuncin tantance ƙungiyar da za ta shiga wasan ƙarshe ta hanyar bugun fenareti.
A bugun fenaretin, Samuel Chukwueze da Bruno Onyemachi sun kasa zura ƙwallo a raga domin Super Eagles, yayin da ‘yan wasan Morocco, Atlas Lions, suka zura dukkan bugun fenaretinsu cikin nasara.
Morocco za ta fafata da Senegal a wasan ƙarshe na gasar, yayin da Najeriya za ta kara da Masar a wasan neman matsayi na uku.
