Tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na Jam’iyyar Labour (LP), Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya bayyana shakku kan yiwuwar Peter Obi samun tikitin takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), yana mai danganta hakan da rikice-rikicen muradu da burace-buracen siyasa da har yanzu ba su warware ba a cikin sabuwar haɗakar jam’iyyun.
A wata hira da ya yi da Trust TV, Datti ya bayyana dalilan da suka sa ya zaɓi ci gaba da zama a Jam’iyyar Labour duk da ficewar Peter Obi, yana mai jaddada cewa Obi bai taɓa gayyatarsa ya shiga ADC ba. Ya kuma ce tsohon gwamnan Jihar Anambra na da ’yancin komawa Jam’iyyar Labour idan aka hana shi tikitin ADC.
Datti ya yi watsi da ra’ayoyin da ke cewa tasirinsa a siyasa ko makomarsa na rataye ne kacokan a kan Peter Obi, yana mai cewa tarihinsa a siyasa ya fara ne tun kafin Obi kuma ya zarce kowane mutum guda.
Wasu masu sukar ra’ayi na cewa Peter Obi shi ne babban ginshiƙin Jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, kuma ficewarsa ta sa jam’iyyar ta rasa tasiri. Sai dai Datti ya ce irin waɗannan maganganu labaran kafafen sada zumunta ne da ba lallai su kasance gaskiya ba.
“Na bayyana a fili cewa ba lokaci ba ne na bayyana wata buri. A rubuce na faɗi hakan. Amma duk da haka mutane suka ce na ayyana aniyar tsayawa takarar shugaban ƙasa. Wannan ba gaskiya ba ne,” in ji shi.
Ya ce dalilin da ya fito fili a wannan lokaci shi ne don sanar da duniya cewa har yanzu yana cikin Jam’iyyar Labour, yana mai cewa bai gamsu da hujjojin da aka bayar na ficewa daga jam’iyyar ba.
“Jam’iyyar Labour ta wanzu tun kafin Peter Obi. Ta samar da gwamnoni kafin zuwansa. Hakika, Obi ya zo da gagarumin goyon bayan Kudu maso Gabas, Arewa ta Tsakiya da Kiristoci a Arewa, kuma hakan ya yi tasiri.
Amma a rayuwa, kana amfana da ƙoƙarin wasu, su ma suna amfana da naka,” in ji Datti.
Da aka tambaye shi ko har yanzu yana hulɗa da Peter Obi da kuma ko Obi ya gayyace shi zuwa ADC, Datti ya ce, “Peter Obi bai gayyace ni shiga ADC ba. Dangantakarmu ta sirri tana nan daram. A ranar 12 ga wata ma ya halarci ɗaurin aure a gidana da kansa.”
Ya ce yana girmama Peter Obi matuƙa, yana mai ƙara da cewa idan Obi bai samu tikitin ADC ba ya kuma yanke shawarar komawa Labour, zai yi aiki tukuru don tabbatar da ya samu tikitin jam’iyyar tare da sulhunta shi da duk wanda yake da sabani da shi.
Datti ya ce a 2023 ya goyi bayan burin Obi na shugaban ƙasa da zuciya ɗaya saboda a wancan lokaci hakan ne ya dace. Ya kuma ce a 2027, dan Arewa na iya zama shugaban ƙasa, yana mai cewa Kudu ne ya fara karya tsarin karɓa-karɓa.
Dangane da ADC, Datti ya ce yawancin mutanen da ke cikinta—ban da Peter Obi—su ne waɗanda suka taimaka wajen kafa APC a 2015.
“Me zai sa na sake faɗawa wannan tarko?” ya tambaya.
Ya ce ko da yake yana girmama mutane irin su Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi, amma ya jaddada cewa ADC ba ta da irin manyan ginshiƙan da suka bai wa APC nasara a 2015 kamar Muhammadu Buhari ko Bola Ahmed Tinubu.
“Waɗannan su ne mutanen da suka ƙirƙiri dodon APC da ke lalata Najeriya a yau. Babu wani abu da ya canza a kansu,” in ji shi.
Kan yiwuwar zaɓin “ƙananan sharri”, Datti ya ce ADC ta fi APC sauƙin sharri, yana mai cewa dawowar Tinubu kan mulki zai zama masifa ga ƙasar.
Da aka tambaye shi ko zai bi Peter Obi idan ya gayyace shi zuwa ADC, Datti ya ce zai ƙi cikin girmamawa. Ya ƙara da cewa yana ganin ba abu ne mai sauƙi ba Obi ya samu tikitin ADC saboda ƙarfin burin manyan ’yan siyasar da ke cikinta, ciki har da Atiku Abubakar, wanda ya riga ya bayyana cewa ba zai janye wa kowa ba.
“Ina ganin yana da wuya Peter Obi ya samu tikitin. Amma idan ya samu, zan yi farin ciki a gare shi,” in ji Datti.
Ya kuma yi watsi da ra’ayin karɓar takarar mataimakin shugaban ƙasa, yana mai cewa duk manyan ’yan takarar ADC na son zama shugaban ƙasa ne, ba mataimaki ba.
Datti ya ce APC ba jam’iyya ce mai firgitarwa ba, yana mai jaddada cewa idan hukumomi irin su INEC, DSS da ’yan sanda suka yi aiki bisa gaskiya a 2027, APC za a kayar da ita tun kafin tsakar rana.
Dangane da masu cewa Jam’iyyar Labour tana nutsewa, Datti ya ce babu wata jam’iyya a Najeriya da ba ta da matsala. Ya ce APC, PDP da ADC duk suna fuskantar ƙalubale iri-iri.
“Jam’iyyar Labour tana da aminci. A nan na zaɓi inganta haɗin kan ƙasa. A 2023 na yi aiki don ganin ɗan Kudu maso Gabas ya zama shugaban ƙasa,” in ji shi.
Ya ƙare da cewa bai dogara da kowa ba wajen samun nasara a siyasa, yana mai cewa bai taɓa shan kaye a zaɓe ba a rayuwarsa.
“Idan yin iyo saɓanin rafi ne ake buƙata, na shirya,” in ji Datti.
Labari: Daily Trust









