Trends

An Bai wa Kamfanonin Sadarwa da Bankuna Wa’adin Mayar da Kuɗin Airtime

Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) tare da Babban Bankin Najeriya (CBN) sun bai wa kamfanonin sadarwa da bankuna wa’adin zuwa ranar 1 ga Maris, 2026, domin fara aiwatar da sabon tsarin mayar da kuɗi ga kwastomomi idan aka samu tangarda wajen sayen airtime ko data.

Hukumomin biyu sun samar da wannan tsari ne domin magance yawan ƙorafe-ƙorafen masu amfani da layukan sadarwa, musamman kan matsalar cire kuɗi ba tare da samun airtime ko data ba.

Daraktar kula da harkokin masu amfani da NCC, Misis Freda Bruce-Bennett, ta ce matsalar sayen kati ko data da bai yi nasara ba na cikin manyan ƙorafe-ƙorafe uku da hukumar ke samu. Ta ce, “Matsalolin caji da bai yi nasara ba na daga cikin manyan ƙorafe-ƙorafen da muke samu, kuma mun kuduri aniyar magance su cikin gajeren lokaci.”

Sabon tsarin ya tanadi kafa wani Cibiyar Sa-ido ta Tsakiya (Central Monitoring Dashboard) da za ta rika bibiyar mayar da kuɗaɗe da kuma sa ido kan karya yarjejeniyar ingancin aiki (SLA). Haka kuma, an samar da SLA mai ƙarfi da za a tilasta aiwatarwa ga kamfanonin sadarwa (MNOs) da kuma bankunan kasuwanci (DMBs).

A ƙarƙashin sabon tsarin, idan an cire kuɗi amma ba a samu airtime ko data ba, za a mayar da kuɗin cikin sakan 30. Idan kuma aka samu jinkiri, to cikin awa 24 za a warware matsalar gaba ɗaya.

Rahotanni sun nuna cewa sama da naira biliyan 10 tuni aka mayar wa kwastomomi sakamakon irin waɗannan matsaloli a baya. Haka kuma, masu amfani za su rika samun saƙon SMS da ke nuna ko ciniki ya yi nasara ko ya fadi, tare da ɗaukar mataki kan matsaloli kamar caji da aka tura wa lamba ba daidai ba.

Za a fara aiwatar da sabon tsarin daga ranar 1 ga Maris, 2026, bayan samun cikakkun amincewa da kuma kammala haɗa tsarin fasaha da ya dace.