Tsohon ministan sadarwa na Najeriya, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya janye daga zaɓen fitar da gwani na gwamnan Gombe na jam’iyyar APC.
Cikin wani saƙo da Farfesa ya wallafa a shafukansa na sada zumunta ya ce ya ɗauki matakin ne bayan zargin jam’iyyar da karya dokar zaɓe da kuma rashin bin ƙa’idojin gudanar da zaɓen.
Farfesa Pantami ya ce ya fice daga zaɓen fitar da gwanin da ake sa ran gudanarwa ranar 21 ga Mayu “cikin nuna rashin amincewa da tsarin da aka yi”.
Ya ci gaba da cewa shugabannin jam’iyyar sun kasa yin bayani a kan yadda aka tsara zaɓen cikin aminci.
Ya ce an yi watsi da buƙatun da ya gabatar domin neman bayanai kan yadda za a tantance wakilai, da tsarin kaɗa ƙuri’a da wuraren tattara sakamako.
Pantami ya bayyana cewa ya ɗauki matakin ne bayan tuntuɓa da magoya baya da masu ruwa da tsaki, sakamakon abin da ya kira rashin gaskiya da kura-kurai a zaɓen fitar a gwani na ‘yan takarar majalisar dokoki da APC ta gudanar a jihar kwanan nan.

