Obi Ya Zama Dan Takarar Shugaban Kasa Kadai Na NDC

Kwamitin tantance ‘yan takara na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ya tantance tare da amincewa da Peter Obi domin tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027.

An tantance Obi ne a ranar Laraba a matsayin dan takarar shugaban kasa guda daya tilo gabanin zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party ya isa hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja da misalin karfe 6:45 na yammacin ranar Talata, tare da rakiyar Sanata Victor Umeh mai wakiltar Anambra ta Tsakiya.

Kwamitin tantancewar wanda tsohon ministan ilimi, Sam Egwu, ke jagoranta ne ya yi wa Obi tambayoyi yayin tantancewar.

Egwu ya bayyana cewa kwamitin ya gamsu da yadda Obi ya amsa tambayoyin da aka yi masa, yana mai cewa tsohon gwamnan jihar Anambra ya amsa dukkan tambayoyin yadda ya kamata.

Daga bisani, Egwu ya mika wa Obi takardar shaidar amincewa tare da fom din takarar jam’iyyar mai lamba 001.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *