Daga Segun Adebayo
Bayanan Haraji su ne Zuciyar Tattalin Arziƙinmu, kuma babu wata ƙasa da za ta mika zuciyarta ga wani ta kuma yi tsammanin za ta ci gaba da kasancewa mai cikakken ‘yanci.
Jiya ne Hukumar Tara Haraji ta Ƙasa (FIRS) ta sanya hannu kan yarjejeniyar fahimta (MoU) da Hukumar Haraji ta Faransa (Direction Générale des Finances Publiques – DGFiP), inda hakan ke bai wa ɗaya daga cikin ƙwararrun hukumomin haraji na Turai damar yin aiki kai tsaye kan tsarin harajin dijital na Najeriya. Duk da cewa ana ta bayyana alfanun wannan yarjejeniya a jaridunmu, yana da muhimmanci mu fahimci cewa wannan ba wata haɗin gwiwa ce ta fasaha kawai ba; a’a, shi ne sabon kuma mafi hatsarin mataki a cikin dogon yunƙurin da wasu ƙasashen waje ke yi na samun iko kan bayanan harajin Najeriya masu alaƙa da ‘yancin ƙasa.
Na yi gargaɗi kan wannan yanayi tun watanni tara da suka wuce a cikin jawabin bude taro na mai taken “Kare ‘Yancin Bayanai na Haraji” a Taron Jin Ra’ayoyi kan Gyaran Haraji da Matasa a Majalisa suka shirya a watan Maris, 2025.
A cikin jawabin na bayyana cewa: “Najeriya ƙasa ce mai ƙarfin fasahar kuɗi (fintech). Muna da kamfanoni irin su Flutterwave, PayStack, Interswitch, PiggyVest, Bamboo, NIBSS — muna jagorantar Afirka wajen kirkire-kirkire da amfani da intanet. Babbar dukiyarmu ita ce mutanenmu. Amma duk da haka, wasu ƙasashen waje na zagaye suna bayar da ‘taimako’ wanda a ƙarshe ke kawo barazana ga ‘yancin tattalin arziƙinmu. Bayanai na masu biyan haraji iko ne na ƙasa. Ba wa ƙasashen waje damar sarrafa waɗannan bayanai barazana ce ga tsaron ƙasa.”
A jawabin da na yi a dakin manema labarai na Majalisar Dattawa a ranar 26 ga Maris, 2025, na bayyana wa manema labarai cewa duk ƙasar da ta ba wa ƙasashen waje bayanan harajinta, tamkar ta ba baƙo makullin gidanta ne har ma da ɗakin kwana.
Wannan ya biyo bayan ganawa da Sanata Ned Munir Nwoko kan gyara kudirin Dokar Kare Bayanai ta Najeriya (Gyara) ta 2025 (SB 650), inda na ba da shawarar a ƙara sabbin sashe da za su kare bayanan kuɗi da na wurin mutum (GPS) a matsayin bayanan sirri masu matuƙar muhimmanci, tare da samar da ƙa’idoji na kare bayananmu daga mamayar ƙasashen waje. Sanata Ned Nwoko ya saurara da kulawa, tare da umartar tawagarsa da su ci gaba da tattaunawa yayin da ake shirin taron jin ra’ayoyi kan kudirin.
Abin takaici, kudurorin gyaran haraji sun wuce ba tare da waɗannan kariya ba, kuma yanzu ga wannan yarjejeniya (MoU) ta zo ba tare da cikakken bincike ba.
Babu wata ƙasa da ke bayar da taimako kyauta; duk suna neman wata fa’ida daga raunanan tattalin arziƙinmu. Idan Faransa ta sami damar tantance sassan tattalin arziƙin da ke bunƙasa ko waɗanda ke durƙushewa, za su iya tasiri kan kasuwanci, zuba jari da tattaunawar yarjejeniyoyi ta yadda zai amfane su. Me ya sa aka kauce wa manyan kamfanoninmu na cikin gida.
Fassara: Umar M. Gombe

