Farashin Man Fetur Zai Sauka Zuwa ₦739 Daga Talata — Dangote

Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya sanar da cewa farashin man fetur zai sauka zuwa ₦739 kowace lita a fadin Najeriya daga ranar Talata, inda za a fara aiwatarwa a gidajen mai na MRS a Legas.

Dangote ya bayyana hakan ne a taron manema labarai da aka gudanar a Matatar Dangote da ke Lekki a ranar Lahadi, inda ya ce matatar ta rage farashin gantry daga ₦828 zuwa ₦699 kowace lita tun kwanaki biyu da suka gabata.

Ya tabbatar da cewa za a aiwatar da farashin ₦739 tare da jaddada kudurinsa na yaki da duk wani yunkuri na tashin farashi da yaudara.

“Daga Talata, MRS za ta fara sayar da man fetur a ₦739/lita. Lallai za mu tabbatar da an aiwatar da wannan farashi. Za mu tabbatar an aiwatar. Idan kana da mota (tanker), za ka iya zuwa ka saya a nan. Muna sayarwa a ₦699. Wannan ₦699 ya hada da kaso na NMDPRA. Abin da ya rage mana a zahiri kusan ₦389 ne,” in ji shi.

Ya kara da cewa: “Wadanda ke son ci gaba da rike farashi don su yi wa gwamnati zagon kasa, za mu yi yaki da su gwargwadon iko domin a rage farashin. ₦970 ba farashin gaskiya ba ne. Idan kana da kudi ka zo ka saya, za ka iya daukar man fetur a ₦699.”

Shugaban rukunin ya nuna damuwa cewa wasu gidajen mai na rike farashi da gangan, suna hana saukin da ake son cimmawa.

“An fada min cewa ‘yan kasuwa sun hadu da [wasu jami’ai] kuma an ce su tabbatar da farashin ya ci gaba da tsada. Amma farashin da za mu gabatar, za mu fara da gidajen MRS, mafi yiyuwa daga Talata a Legas; ₦970 kowace lita ba za ku sake gani ba,” in ji Dangote.

Dangote ya bukaci mambobin Independent Petroleum Marketers Association of Nigeria (IPMAN) da sauran masu saye su rika sayen man fetur a farashin gantry na ₦699.

“Mun bukaci duk wanda zai iya sayen tankoki 10 ya zo ya saya tankoki 10 a ₦699. Za mu yi amfani da dukkan albarkatun da muke da su domin mu karya farashin kasa.

“Cikin mako guda zuwa kwana 10, za mu iya kaiwa. A wannan Disamba da Janairu, ba ma son a rika sayar da man fetur sama da ₦740 a duk fadin kasa,” ya bayyana.

Dangote ya kuma bayyana cewa kudin jigilar man fetur daga matatar bai wuce ₦15 kowace lita ba, yana tambayar dalilin da ya sa farashin famfo ke tashi har zuwa ₦900.

“Jigila a cikin Legas ₦10 zuwa ₦15 ne, mafi yawa. Don haka idan ₦10 zuwa ₦15 ne, dukkanin kudin zai zama ₦715. Me ya sa za ka sayar a ₦900? Ya kamata mutane su samu farashin gaskiya,” in ji shi.

Har ila yau, ya soki Hukumar Kula da Harkokin Tsakiya da Kasan Man Fetur ta Najeriya (NMDPRA) kan bayar da lasisin shigo da man fetur 47 da suka kai sama da lita biliyan 7.5 na zangon farko na shekarar 2026.

Dangote ya ce irin wannan mataki na hana zuba jari a cikin gida tare da barazana ga kananan (modular) matatun mai.

“Suna yawan bayar da lasisi a tsakiyar wata. Yanzu kuma sun shirya bayar da lasisi na kusan lita biliyan 7.5 na zangon farko na 2026, duk da cewa mun tabbatar za mu wadatar da kasuwa.

“Wadannan kananan matatun mai kusan suna dab da durkushewa. Babu wanda ke samun riba,” in ji shi.