Rundunar ’yan sanda ta jihar Delta ta kama wata mata mai shekaru 21 mai suna Lilian, bisa zargin daba wa abokin zamanta mai shekaru 34 wuka har lahira a lokacin rikicin cikin gida.
Kakakin ’yan sandan jihar, Bright Edafe, ya bayyana cewa Lilian ta fara zaune da mamacin tun tana da shekaru 17, kuma suna da ’ya’ya biyu tare bayan shekaru huɗu da zama.
Rikicin ya fara ne lokacin da Lilian ta roƙi abokin zamanta ya taimaka ya saka kudin lantarki a mita, amma ya yi biris da ita. Wannan ya jawo cece-kuce, inda ya bugi Lilian da bulala sannan ya buga kanta da ƙasa.
A cikin tsananin tsoro, Lilian ta nufi ɗakin girki ta ɗauki wuka ta soka masa a kirji lokacin da ya taso kanta. Ta bayyana cewa ta yi hakan ne wajen kare kanta, tana ikirarin cewa mamacin ya nemi kawo ƙarshen dangantakarsu, lamarin da ya jawo tashin hankali.
Lilian ta nuna nadama inda ta ce: “Ba na farin ciki cewa ya rasu.”
’Yan sanda sun tabbatar da cewa za a gurfanar da Lilian bisa laifin kisa. Edafe ya shawarci ’yan Najeriya da su riƙa daurewa da kuma sarrafa fushinsu don kauce wa irin waɗannan mummunan abubuwa.
Haka kuma ya yi tambaya kan dalilan zamantakewa da suka fara zama tun da wuri da kuma nauyin iyaye wajen irin waɗannan matsalolin.



