Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ta bayyana cewa ta cafke kwalaben Akuskura guda dubu takwas (8,000) tare da buhunan tabar wiwi guda 48 a jihar Kano.
Akuskura wani hadin ganye ne da ake zargin na dauke da kwayoyi masu hadari, wanda ake amfani da shi sosai a Arewacin Najeriya.
Mai magana da yawun NDLEA a Kano, Sadiq Muhammad-Maigatari, ne ya bayyana hakan a cikin wani faifan bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta.
Ya ce jami’an hukumar sun cafke tirelar ne a kusa da Gadar Tamburawa, hanyar Zaria–Kano, wacce take dauke da kayan daga Legas zuwa Maiduguri.
Sadiq ya kara da cewa an kama wani mutum mai shekaru 37 mai suna Ali Muhammad a cikin lamarin.
Ya ce kwalaben Akuskura 8,000 da kilo 408 na tabar wiwi an gano su a boye a karkashin bene na tirela. An gina wata bunkera ta boye a karkashin bene tare da shimfida katakon itace domin ɓoye kayan.
A cewarsa: “Duk da dabarar da aka yi da katako da kuma buhunan garin gawayi don rufe kayan, jami’anmu sun gano su. Wannan bene ya yi kama da wanda masana’anta suka yi na asali. Amma jajircewar jami’anmu da addu’o’in ku ne suka kai ga gano lamarin.”
Ya kara da cewa ma’aikata sun sha wuya wajen bude bunkerar saboda yadda aka tsara ta cikin basira domin boye kayan.
Dukkan kayan da wanda ake zargi yanzu suna hannun NDLEA domin ci gaba da bincike da gwajin dakin gwaje-gwaje, don tabbatar da irin wadannan kwayoyi da kuma gano girman harkar.
Hukumar NDLEA ta yi kira ga jama’a da su kasance masu lura da kuma bayar da rahoton kowanne kaya ko motsi da ake zargin na da nasaba da miyagun kwayoyi ga ofishin NDLEA mafi kusa ko kuma sauran jami’an tsaro.



