’Yan Najeriya Sun Kashe Naira Biliyan 84 Kan Mitoci a 2025

Masu amfani da wutar lantarki a Najeriya sun biya aƙalla Naira biliyan 84.36 domin sayen mitoci a shekarar 2025 ƙarƙashin shirin Meter Assets Programme (MAP), kamar yadda bayanan Nigerian Electricity Regulatory Commission suka nuna.

Shirin MAP na bai wa kastomomi damar biyan kuɗin mita, sannan kamfanonin rarraba wuta (DisCos) su mayar musu da kuɗin ta hanyar tokens na wuta cikin tsawon shekaru 10.
An yi amfani da matsakaicin farashin Naira 130,000 ga kowace mita wajen ƙididdigar, duk da cewa farashin na bambanta tsakanin masu samarwa, inda mitoci masu layi uku (three-phase) ke wuce Naira 200,000.

Rahoton kwata-kwata na NERC ya nuna cewa an girka mitoci 965,303 a shekarar 2025, mafi yawansu a rabin shekara na biyu. Daga cikin su, 648,972 (kashi 67.23%) sun fito ne ta hanyar MAP, sai 125,025 ta Meter Acquisition Fund (MAF), da kuma 88,553 ƙarƙashin shirin Distribution Sector Recovery Program na Bankin Duniya.

Sauran hanyoyin sun haɗa da mitoci 77,967 da masu kaya suka ɗauki nauyi da kuma 5,892 da kamfanonin rarraba wuta suka biya. Bayanai sun nuna ƙaruwa a kowace kwata, inda aka fi girka mitoci 323,864 a kwata na huɗu (Q4).

Duk da tabbacin gwamnati cewa mitocin DISREP kyauta ne, rahotanni sun nuna ana bai wa kwastomomin Band A fifiko, waɗanda ke biyan kuɗin wuta bisa cikakken farashi. Wani jami’in DisCo a Abuja ya ce, “Muna bai wa Band A fifiko saboda su ne ginshiƙin dorewar kasuwar wuta.”

Sai dai masu amfani da wuta na korafi kan jinkiri da kuma zargin cin hanci wajen rabon mitoci. Wani mazaunin Abuja ya ce ya nema tun watan Janairu amma har yanzu bai samu ba, yana mai cewa wasu sun biya kuɗin hannu domin a hanzarta musu.

Jami’an gwamnati sun dage cewa mitocin DISREP kyauta ne. Shugaban Bureau of Public Enterprises, Ayodeji Gbeleyi, da Shugaban NERC, Musliu Oseni, sun bukaci jama’a da su guji biyan kuɗi, suna mai cewa duk wata karɓar kuɗi ba bisa ka’ida ba na iya fitowa daga masu girka mita ko wasu ma’aikata, ba daga shugabanci ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *