Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin haɗa kula da cutar Haemophilia da sauran cututtukan zubar jini na gado cikin ayyukan kiwon lafiyar uwa da yaro a matakan farko da na sakandare a fadin ƙasa.
Ministan Lafiya da Jin Daɗin Jama’a mai kula da harkokin daidaitawa, Muhammad Ali Pate, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin taron manema labarai na bikin World Haemophilia Day 2026. Ya samu wakilci daga Dr. Kamil Shoretire, inda ya ce shirin na da nufin gano masu cutar da wuri da kuma haɗa su cikin cikakken kulawa.
Pate ya nuna damuwa cewa duk da kimanin ‘yan Najeriya 21,101 na fama da haemophilia, kusan kashi uku cikin ɗari ne kawai aka gano. Ya yi gargaɗin cewa ƙarancin sani game da cutar a tsakanin ma’aikatan lafiya na iya ƙara yawan mace-mace da matsaloli idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba.
Gwamnatin ta kuma ƙaddamar da Rijistar Ƙasa ta Cututtukan Zubar Jini domin inganta tattara bayanai, tare da ƙaddamar da shirin “Road to Clot Initiative” haɗin gwiwa da World Federation of Haemophilia da Haemophilia Foundation of Nigeria.
Shirin zai gano marasa lafiya da ba a tantance ba, ya haɗa su da cibiyoyin jinya, tare da tabbatar da kulawa na dogon lokaci.
Pate ya ce taken bana, Diagnosis: The First Step to Care, ya yi daidai da manufofin ƙasa, yana mai jaddada cewa ingantaccen ganowa shi ne ginshiƙi na samun magani mai tasiri. Ya kuma buƙaci masu ruwa da tsaki su ƙara ƙaimi wajen wayar da kai.
Daraktar zartarwa ta gidauniyar, Megan Buckie Adediran, ta yabawa ma’aikatan lafiya da abokan hulɗa, tana mai cewa ranar na nuna gwagwarmaya da juriyar marasa lafiya.
Haka kuma mataimakiyar shugaba (fannin likitanci), Theresa Nwagha, ta ce wannan shiri babban mataki ne wajen tabbatar da daidaito a kiwon lafiya, tare da gwaje-gwaje a matakin al’umma da ingantattun hanyoyin tantance cuta.
A wani ɓangare na shirin, an ƙaddamar da motocin daukar marasa lafiya guda biyar domin tallafa wa kai agaji a yankunan da ke da wahalar isa. Jami’ai sun ce wannan mataki zai rage nauyin tattalin arziki da zamantakewa na cututtukan zubar jini tare da ƙarfafa tsarin kiwon lafiyar Najeriya.


