Trends

Sama da Likitoci 4,000 Sun Koma Birtaniya Tun 2023 – Rahoto

Kiwon lafiya Kiwon lafiya

Tsarin kiwon lafiyar Najeriya na fuskantar ƙarin matsin lamba bayan da sabbin bayanai daga General Medical Council (GMC) suka nuna cewa likitoci 4,691 sun koma United Kingdom tun bayan hawar Bola Tinubu kan mulki a watan Mayun 2023.

Rahoton ya bayyana cewa wannan ƙaura na wakiltar babbar matsala ta rashin ƙwararrun ma’aikata tare da asarar tattalin arziki. Bisa kiyasin gwamnati cewa horar da likita guda na kashe dala 21,000, Najeriya ta yi asarar aƙalla dala miliyan 98.5 cikin ƙasa da shekaru uku.

Alƙaluman GMC sun nuna cewa jimillar likitocin da aka horar a Najeriya da ke aiki a Birtaniya sun kai kusan 15,692, wanda ya sa Najeriya ta zama ƙasa ta biyu mafi yawan likitocin ƙasashen waje a can bayan Indiya.

Adadin likita zuwa yawan jama’a a Najeriya ya tsaya a 3.9 cikin mutane 10,000, ƙasa da ƙa’idar mafi ƙaranci da World Health Organization ta gindaya, lamarin da ke nuna tasirin ficewar likitocin.

Nigerian Medical Association ta sha bayyana cewa ƙarancin albashi, rashin tsaro a wurin aiki, da ƙarancin kayayyakin aiki ne ke tilasta likitoci barin ƙasar. Ta ce, “Mambobinmu suna aiki fiye da ƙima, ana biyansu ƙasa da yadda ya kamata, kuma suna fuskantar haɗari a kullum.”

Haka kuma National Association of Resident Doctors ta nuna damuwa kan matasan likitoci, tana mai cewa rashin daidaiton albashi, yawan aiki fiye da kima, da rashin damar ƙarin horo na daga cikin manyan dalilan da ke sa su bar ƙasar.

A lokaci guda kuma, yayin da likitoci ke ficewa, Najeriya na ci gaba da kashe kuɗi sosai kan yawon neman magani a ƙasashen waje. Bayanai sun nuna cewa kashe kuɗin ya kai dala miliyan 549.29 a watanni tara na farkon shekarar 2025, daga dala miliyan 465.67 a 2024.
Wani ƙwararren masanin kiwon lafiya, David Adewole, ya ce matakan gwamnati kan ƙaurar ma’aikatan lafiya na da amfani amma ba su isa ba.

Ya jaddada cewa matsalolin tsaro, ƙarancin albashi, fansho marasa tabbas, da rashin muhimman kayayyaki har yanzu na nan, yana mai cewa: “Domin a sa ma’aikatan lafiya su zauna, dole ne albashi ya rufe buƙatun yau da kullum kamar abinci, gidaje da wutar lantarki. Aiwwatarwa ce babban ƙalubale.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *