’Yan Najeriya Sun Kashe Naira Biliyan 84 Kan Mitoci a 2025
Masu amfani da wutar lantarki a Najeriya sun biya aƙalla Naira biliyan 84.36 domin sayen mitoci a shekarar 2025 ƙarƙashin shirin Meter Assets Programme (MAP), kamar yadda bayanan Nigerian Electricity Regulatory Commission suka nuna. Shirin MAP na bai wa kastomomi damar biyan kuɗin mita, sannan kamfanonin rarraba wuta (DisCos) su mayar musu da kuɗin ta…


