‘Yan Kasuwar Mai Sun Yi Watsi da Tsarin Sayar da Fetur da Dala na Matatar Dangote

Ƙungiyoyin masu sayar da man fetur masu zaman kansu da masana harkokin makamashi sun yi watsi da matakin da Matatar Man Dangote ta ɗauka na fara sayar da kayayyakin man fetur da dalar Amurka, suna gargadin cewa hakan na iya ƙara matsin lamba kan musayar kuɗaɗen waje tare da haddasa cikas a ɓangaren kasuwancin man fetur na ƙasa.

A kwanakin baya, matatar ta sanar da cewa daga yanzu duk farashin man fetur, dizal da man jiragen sama da ake sayarwa daga matatar za a bayyana su ne da dalar Amurka, tare da soke duk takardun farashi da aka fitar a baya da naira.

Ƙungiyar Masu Gidajen Sayar da Man Fetur ta Najeriya (PETROAN) ta soki wannan mataki, tana mai cewa zai iya kai Najeriya ga tsarin amfani da dala a ma’amaloli maimakon naira.

Shugaban PETROAN, Billy Gillis-Harry, ya ce wannan mataki na iya mayar da Najeriya ƙasa mai dogaro da dala wajen kasuwanci.

Ya ƙara da cewa manyan kamfanoni sukan yanke shawarar kasuwanci, amma ya kamata irin waɗannan shawarwari su dace da manufofin tattalin arzikin ƙasa.

Ya kuma yi gargadin cewa idan masu kasuwa suka rika sayen man fetur da dala, dole ne su ɗora wa masu amfani da wannan nauyi ta hanyar ƙarin farashi.

A cewarsa, kamar ana cewa duk wanda ya sayi mai da dala shi ma ya sayar wa jama’a da dala, amma ya jaddada cewa hakan ba zai yiwu ba.

Haka kuma, Ƙungiyar Masu Kasuwar Man Fetur Masu Zaman Kansu (IPMAN) ta roƙi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya ci gaba da aiwatar da tsarin musayar ɗanyen mai da naira, tana mai cewa danganta farashin mai da dala zai sa farashin fetur yana yawan sauyawa.

Tuni masu rumbunan ajiya na man fetur suka fara daidaita farashinsu. A Fatakwal (Port Harcourt), farashin litar fetur ya ƙaru da naira 113, yayin da dizal ya ƙaru da naira 150 kan kowace lita.

Haka kuma an samu irin wannan ƙarin farashi a Legas da Warri, yayin da masu kasuwa suka fara lissafa sabon tsarin farashin da matatar ta ƙaddamar.

Masana harkokin makamashi sun bayyana ra’ayoyi mabambanta kan lamarin.

Farfesa Wumi Iledare ya ce matakin da Matatar Dangote ta ɗauka wata dabara ce ta kasuwanci domin kare kanta daga haɗarin sauyin darajar kuɗaɗen waje.

Ya bayyana cewa daidaita kuɗaɗen shiga da manyan kuɗaɗen da kamfani ke kashewa hanya ce ta gudanar da haɗarin kasuwanci, kuma bai kamata a ɗauki hakan a matsayin tsarin farashi da bai dace ba.

Sai dai Farfesa Dayo Ayoade na Jami’ar Legas (UNILAG) ya ce duk wata ma’amala da ake yi a cikin Najeriya ya kamata ta kasance da naira, domin ita ce halastacciyar kuɗin ƙasar. Ya kuma bukaci hukumomin da ke kula da harkokin man fetur su sake duba wannan sabon tsari.

Masu ruwa da tsaki a masana’antar sun bayyana cewa duk da irin gudunmawar da Matatar Dangote ta bayar wajen tabbatar da wadatar man fetur a ƙasa, ya zama wajibi hukumomin da abin ya shafa su tabbatar da akwai adalci a gasa tsakanin masu kasuwanci tare da kare muradun masu amfani da kayayyakin man fetur.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *