Ministan Kuɗi Ya Ƙaddamar da Kwamitin Ba da Shawara kan Tattalin Arziki

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da Kwamitin Ba da Shawara ga Minista kan Tattalin Arziki, domin ƙarfafa tsara manufofin tattalin arziki, inganta haɗin kai tsakanin hukumomi, da kuma hanzarta aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki da harkokin kuɗi.

An ƙaddamar da kwamitin ne a Abuja ta hannun Ministan Kuɗi kuma Ministan da ke Kula da Tattalin Arzikin Ƙasa, Taiwo Oyedele, wanda ya ce kwamitin zai ba gwamnati shawarwari masu zaman kansu da suka dogara da hujjoji domin taimakawa wajen hango barazanar tattalin arziki tun kafin su rikide zuwa manyan matsaloli, tare da tabbatar da cewa sauye-sauyen da ake aiwatarwa suna amfani ga al’umma.

Ya ce tattalin arzikin Najeriya na da sarkakiya, yayin da damar gwamnati ta fuskar kuɗaɗe ke da ƙalubale. Saboda haka, an kafa kwamitin ne domin ba da shawarwari masu amfani daga waje, gano raunana kafin su zama matsala, da kuma tantance yadda sauye-sauyen gwamnati ke tasiri ga masana’antu, ‘yan kasuwa da al’ummomi.

Kwamitin mai mambobi 15 na ƙarƙashin jagorancin Abubakar Suleiman, Manajan Daraktan Sterling Bank, kuma ya ƙunshi masana tattalin arziki, shugabannin kamfanoni da ƙwararrun masana manufofin gwamnati.

Ayyukan kwamitin za su mayar da hankali kan manyan fannoni huɗu, waɗanda suka haɗa da:

  • Ba da shawara kan manufofin tattalin arziki, musamman batutuwan bunƙasar tattalin arziki, samar da ayyukan yi, haɓaka yawan aiki da ƙara kuɗaɗen shiga.
  • Inganta yadda ake gudanar da kuɗaɗen gwamnati, da suka haɗa da ladabtar da kashe kuɗi, sarrafa bashin gwamnati da tabbatar da gaskiya.
  • Ƙarfafa haɗin kai tsakanin ma’aikatun gwamnati da ɓangaren masu zaman kansu wajen aiwatar da manufofi.
  • Tabbatar da cewa sauye-sauyen tattalin arziki suna haifar da ingantuwar rayuwar ‘yan Najeriya.

Da yake jawabi a madadin kwamitin, shugabansa Abubakar Suleiman ya yi alƙawarin bayar da shawarwari masu amfani da za su taimaka wa gwamnati.

Ya ce aikin kwamitin shi ne ya ba ma’aikatar damar mayar da hankali kan gudanar da ayyukanta, yayin da su kuma za su nazarci batutuwan da ba a fara dubawa ba, tare da kawo shawarwarin da suka samo asali daga damuwar ‘yan Najeriya.

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da Dakta Ayo Teriba, Farfesa Uche Uwaleke, Chinyere Almona, Vincent Nwani, Segun Oloketuyi, Jide Adeola, Dimeji Salaudeen, Damilola Akinbami, Idris Belo-Osagie, Injiniya Jani Ibrahim, Segun Ajayi-Kadri, Farfesa Joseph Nnanna, Dakta Suleyman Ndanusa, da Dakta Baba Yusuf Musa.

Ana sa ran kwamitin zai taimaka wa gwamnati wajen ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki, ƙarfafa tsarin kula da kuɗaɗen gwamnati, da kuma bunƙasa tattalin arziki mai amfanar kowa a faɗin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *