Bankin Masana’antu na Najeriya (BoI) ya ƙaddamar da wani asusun tallafi na Yuro miliyan 85 domin bunƙasa masana’antar sarrafa koko a ƙasar, rage dogaro da fitar da ɗanyen koko zuwa ƙasashen waje, tare da ƙara darajar kayayyakin koko a cikin gida.
Da yake sanar da shirin a taron Cocoa Value Addition Summit 2026 da aka gudanar a Abuja, Manajan Daraktan BoI, Dakta Olasupo Olusi, ya ce bankin ya fi mayar da hankali kan ƙara darajar amfanin gona a cikin gida maimakon fitar da su a matsayin ɗanyen kaya.
Olusi ya ce harkar koko na samar da abin dogaro ga dubban ‘yan Najeriya, kuma ta hanyar wannan shiri bankin na da burin ƙara yawan amfanin da ake samu, inganta sarrafa koko, da faɗaɗa kasuwanni domin ƙara kuɗaɗen shiga na manoma da masu sarrafa koko.
An samar da wannan asusun ne tare da haɗin gwiwar Bankin Zuba Jari na Turai (EIB) da kuma tallafin shirin Global Gateway na Tarayyar Turai (EU).
A cewarsa, kusan kashi 70 cikin 100 na kuɗaɗen za a karkata su ne zuwa ɓangarorin koko da madara, waɗanda aka bayyana a matsayin fannoni masu babban damar samar da ayyukan yi da kuma taimakawa wajen riƙe kuɗaɗen musayar ƙasashen waje a cikin Najeriya.
Olusi ya bayyana cewa Najeriya na rasa kuɗaɗe masu yawa saboda fitar da ɗanyen koko maimakon sarrafa shi zuwa kayayyaki irin su cakulan.
Ya ce idan an sarrafa koko a cikin gida, ana iya samun kuɗaɗen shiga da suka kai dala 30,000 kan kowace tan, idan aka kwatanta da kusan dala 9,000 kan kowace tan da ake samu daga fitar da ɗanyen koko.
Ya ƙara da cewa BoI za ta kuma ba kamfanoni tallafin fasaha domin su cika ƙa’idojin inganci da dorewar muhalli na ƙasa da ƙasa, ciki har da bin Dokar Tarayyar Turai Kan Hana Sare Dazuzzuka (EUDR).
Bankin ya kuma shirya buɗe hanyoyin ba da rance ga ƙananan manoma da ke cikin ƙungiyoyin haɗin gwiwa, ta hanyar ba su rance mai sauƙin ruwa domin sauƙaƙa samun jari da kuma ƙarfafa gina masana’antun sarrafa koko a yankunan da ake nomansa.
Da yake wakiltar Ma’aikatar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari ta Tarayya, Dakta Chris Isokpunwu ya ce har yanzu fiye da kashi 80 cikin 100 na kokon Najeriya ana fitar da shi ne a matsayin ɗanyen kaya.
Ya ce faɗaɗa sarrafa koko a cikin gida zai ƙara kuɗaɗen shiga, samar da ayyukan yi, tare da bunƙasa masana’antu irin su na kayan zaki, kayan kwalliya da kuma magunguna.
Wannan shiri na zuwa ne a lokacin da farashin koko a kasuwannin duniya ke ci gaba da sauyawa. Bayan da farashin ya kai kusan dala 11,000 kan kowace tan a shekarar 2025, ya sauka zuwa kusan dala 4,197 a watan Fabrairun 2026, kafin daga bisani ya sake tashi da kashi 24 cikin 100 a watan Mayu.






