Naira Tiriliyan 5.3: Majalisar Wakilai na Binciken CBN da NNPCL

Kwamitin Kula da Asusun Gwamnati na Majalisar Wakilai ya ƙara tsananta bincikensa kan kuɗaɗen shiga da ba a mayar wa gwamnatin tarayya ba, inda ya umarci Ofishin Akanta Janar na Tarayya (OAGF) da ya gabatar da cikakken bayani kan rarar kuɗaɗen gudanarwa da ake zargin Babban Bankin Najeriya (CBN) da Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL) da sauran hukumomin gwamnati ke bin gwamnati.

‘Yan majalisar sun kuma nuna damuwa kan rahotannin da ke cewa Ofishin Akanta Janar ya cire biliyoyin nairori daga asusun wasu hukumomin gwamnati, ciki har da Hukumar Ilimin Bai Daya ta Kasa (UBEC), inda aka ce an cire naira biliyan 15, lamarin da suka ce ka iya rage wa hukumomin ƙarfin gudanar da ayyukansu.

Ɗaya daga cikin mambobin kwamitin, Gboyega Isiaka, ya soki yadda wasu hukumomi ke kasa mayar da kuɗaɗen da ya kamata su mayar wa gwamnati.

Ya ce, kamfanonin gwamnati ana sa ran su mayar da kusan kashi 80 cikin 100 na rarar kuɗaɗen gudanarwarsu, yayin da wasu hukumomi ke mayar da tsakanin kashi 20 zuwa 50 cikin 100. Sai dai ya ce, daga abin da kwamitin ke gani, har yanzu akwai tarin kuɗaɗen da ba a mayar ba.

Daraktan Sashen Kuɗaɗen Shiga na OAGF, Makinde Mogaji, ya bayyana cewa CBN na bin gwamnati naira tiriliyan 5.3 na rarar kuɗaɗen gudanarwa da bai mayar ba. Ya ce duk ƙoƙarin da aka yi na karɓo kuɗin bai yi nasara ba.

Sai dai ya yaba wa wasu hukumomi kamar Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN), wadda ya ce ta mayar wa gwamnati naira biliyan 473.

A nasa jawabin, Akanta Janar na Tarayya, Shamseldeen Ogunjimi, ya kare tsarin cire kuɗi kai tsaye daga asusun hukumomin gwamnati.

Ya ce wannan hanya ce ta karɓar kuɗaɗen da gwamnati ke da haƙƙi a kansu tun da wuri, kuma hakan ya taimaka wajen samar wa gwamnati kuɗaɗen shiga masu yawa a shekarar da ta gabata.

Sai dai Shugaban Kwamitin, Bamidele Salam, ya ce kwamitin ya karɓi koke daga UBEC da Hukumar Kula da Kimiyya da Injiniya ta Kasa (NASENI) da wasu hukumomi, waɗanda ke zargin cewa an cire kuɗaɗe daga asusunsu ba tare da an mayar musu ba.

A cewarsa, UBEC ta yi ikirarin cewa an cire naira biliyan 16 da kuma wani naira biliyan 15 daga asusunta ba tare da an dawo mata da su ba.

Ya ce hukumomin gwamnati ba za su iya gudanar da ayyukan da doka ta ɗora musu ba yadda ya kamata idan ana karkatar da kuɗaɗensu.

Sai dai Ogunjimi ya dage cewa kuɗaɗen da aka cire an karɓe su ne a matsayin rance na ɗan lokaci domin biyan buƙatun gaggawa na gwamnati. Ya ce akwai lokutan da aka mayar da irin waɗannan kuɗaɗe, ciki har da naira biliyan 300 da aka mayar wa Asusun TETFund.

Duk da haka, ‘yan majalisar sun nuna shakku kan ko wannan tsari ya dace da doka da kuma ko zai iya dorewa.

A ƙarshe, kwamitin ya umarci Ofishin Akanta Janar na Tarayya da ya gabatar da cikakkun bayanai kan duk rarar kuɗaɗen da ba a mayar ba, kuɗaɗen da aka cire, waɗanda aka mayar da kuma sauran ma’aunai, yayin da ake ci gaba da bincike kan bin Dokar Alhakin Gudanar da Kuɗaɗen Gwamnati (Fiscal Responsibility Act) da kuma sahihancin cire kuɗaɗe daga asusun hukumomin gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *