Masu Sayar da Man Fetur Sun Yi Fatali da Karar Dangote Kan Shigo da Fetur
Sabuwar takaddama ta barke a bangaren kasuwancin mai a Najeriya, inda dillalan mai da masu ajiye fetur suka yi watsi da karar da matatar Dangote Petroleum Refinery ta shigar kotu kan batun hana shigo da fetur daga kasashen waje. Matatar ta garzaya Babbar Kotun Tarayya da ke Legas tana neman a soke lasisin shigo da…
