Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Sanata George Akume, ya bayyana damuwa kan ayyukan wasu kungiyoyin masu damfara da ke amfani da fasahar kwaikwayon murya don damfarar manyan mutane da sunan bada mukaman gwamnati.
A wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Yomi Odunuga, ya fitar, SGF ya bayyana cewa “Bisa bayanan da ke hannun ofishinsa, wadannan ’yan damfara sun kwaikwayi muryar SGF suna amfani da ita wajen neman kudi daga mutane da sunan samun mukaman gwamnati.”
Sanata Akume ya nesanta kansa da duk wata alaka da wadannan masu zamba, yana mai cewa ba wai kawai sun kwaikwayi muryarsa ba, har ma sun kwaikwayi lambobin waya na wasu manyan mutane don su yaudari jama’a su aika musu da kudi.
Ya ja hankalin jama’a da su yi hattara da irin wadannan dabarun yaudara, inda ya bayyana cewa dabarar ‘yan damfaran ita ce su yi wa mutum bayani cewa sun samu mukami a gwamnatin tarayya amma sai sun biya kudi domin kammala tsarin.
“Wannan gargadi ya zama dole domin ofishin SGF ya cika da tambayoyi daga jama’a dangane da ayyukan wadannan masu damfara,” in ji sanarwar.
Odunuga ya kara da cewa ’yan damfarar na aikawa da sakonni dauke da bayanan asusun banki inda suke bukatar a ajiye kudi tsakanin naira miliyan 5 zuwa miliyan 15, tare da umarnin a tura CV din mutum zuwa wani adireshin imel da suka kwaikwaya.
Sanata Akume ya jaddada cewa duk wani tsarin nada mukami a hukumomin gwamnati da kwamitoci yana tafiya ne cikin gaskiya da gaskiya, ba tare da sai an biya kudi ba.
“Wasu daga cikin asusun da ’yan damfarar ke amfani da su na cikin sabbin bankuna da kuma fitattun kamfanonin hada-hadar kudi na zamani (fintech) da ke aiki a kasar,” in ji sanarwar.
A karshe, ofishin SGF ya bayyana cewa an riga an sanar da hukumomin tsaro da suka dace game da batun, tare da kira ga ‘yan Najeriya da su rika kai rahoton irin wadannan ayyukan damfara ga hukumomin tsaro, kuma su dauki duk matakan kariya domin gujewa fadawa tarkon masu yaudara.
