Fushi da bakin ciki sun mamaye titunan Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, a ranar Alhamis, yayin da daruruwan mata mafi yawancinsu dattijai da masu shayarwa suka gudanar da zanga-zangar lumana don nuna damuwarsu kan hare-haren ‘yan bindiga da ke ci gaba da kashe mutane, sace su da kuma korar su daga gidajensu.
Rahotanni sun nuna cewa masu zanga-zangar sun fito ne daga kauyen Jimrawa da ke cikin karamar hukumar Kaura Namoda, inda suka yi tattaki zuwa fadar gwamnatin jihar da ke Gusau, suna neman daukin gaggawa don dakile wannan matsalar tsaro da ke kara ta’azzara.
Wannan zanga-zanga ta zo ne makonni biyu bayan wata irinta da aka gudanar a cikin Gusau LGA, inda mazauna suka bayyana cewa sama da rayuka 100 ne suka salwanta a wurare kamar Mada, Ruwan Bore, Fegin Baza, Lilo, Bangi da sauran kauyuka.
“Mun gaji. Mijinmu na hannun ‘yan bindiga, yarinyarmu na fama da yunwa. Ba za mu koma gida ba sai mun samu tabbacin tsaro,” in ji Maimuna Adamu, daya daga cikin masu zanga-zangar.
Wani mai zanga-zanga mai suna Auwalu Umar ya fashe da kuka yana bayyana yadda ‘yan bindiga suka kashe duka iyalinsa. “Sun kashe min uba, uwa, ‘yan’uwa maza da mata. Ina rayuwa shi kadai yanzu, babu tallafi, babu fata,” in ji shi.
Wasu dattijai mata sun zargi ‘yan siyasa da barin jama’a cikin wahala bayan nasarar zabe.
“Mun kada kuri’a wa Gwamna Dauda Lawal da fata cewa za a samu sauyi a harkar tsaro. Amma har yanzu komai ya tsaya cik,” in ji wata mata da ta nemi a boye sunanta.
A cewar hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Jimrawa na daga cikin unguwanni shida da za a yi zaben cike gurbi a ranar 16 ga Agusta. Sai dai mazauna yankin sun ce tabarbarewar tsaro na iya kawo tsaiko, domin masu kada kuri’a da dama ko dai suna cikin daji ko kuma ‘yan gudun hijira ne.
“Kauyukanmu sun zama kufai. Muna rayuwa cikin fargaba. Ba wanda ya san wa ne zai biyo baya,” in ji wani mazaunin yankin.
Rahotanni daga jama’a da dama sun tabbatar da cewa hare-haren ‘yan bindiga sun tsananta a Zamfara kwanan nan, musamman a kauyukan Sabon Garin Damri, Dakko Butsa, Tungar Abdu Dogo, Tungar Sarkin Daji, Sadeda da Tungar Labi, wadanda ke fama da hare-hare masu tsanani.
“Su kan kai hari da dare ko lokacin ruwan sama, lokacin da kowa ke bacci. Ba ma iya noma yanzu,” in ji wani mazaunin Anka LGA.
A kauyen Kadeddaba, mutane 50 na cikin daji, ciki har da mutum 42 da aka sace daga Sabon Gari a kwanakin baya. Mazauna yankin sun ce sojojin da ke kusa ba su dauki mataki ba duk da cewa sun san inda ‘yan bindigar suke.
A kalla mutane shida aka kashe, wasu 45 mafi yawancinsu mata da yara aka sace yayin wani harin hadin gwiwa da ‘yan bindiga suka kai a kauyuka biyar da ke Bakura LGA, ciki har da Sabongarin Damri, Sade, Tungar Tsalle, Tungar Musa Dogo da Tungar Sodangi.
Mazauna sun ce hare-haren sun biyo bayan kin biyan kudin “haraji” da ‘yan bindiga suka dora musu.
“Mun yi taro muka amince ba za mu biya ba. Amma wasu kauyuka sun ci amanar sauran suka biya a boye. Da zarar wa’adin ya cika, sai suka afka wa wadanda suka ki biya,” in ji wani mazaunin yankin.
Wasu daga cikin wadanda aka sace sun samu nasarar tserewa, amma da dama har yanzu na tsare. Wasu matasan gari sun kwato shanun da aka sace bayan fafatawa da ‘yan bindiga yayin da suke janyewa.
An alakanta hare-haren da wani shahararren shugaban ‘yan bindiga da ake kira “Black” wanda ake cewa yana da sansani a dajin Sobubu da ke hada Bakura da wasu sassan jihohin Sokoto da Kebbi.
An bayyana Black a matsayin mai taurin rai kuma mai dauke da muggan makamai. Ana zarginsa da zama ummul haba’isin yawaitar tashe-tashen hankula a Zamfara da kewaye.
Kakakin gwamnatin Zamfara, Mahmud Mohammed Dantawasa, ya tabbatar da kai hare-haren ga BBC, yana mai cewa gwamnati na aiki tukuru don magance lamarin.
Sai dai jama’a da dama sun bayyana rashin gamsuwa. “Ba mu ga wani mataki ba. ‘Yan bindiga su ne ke mulki yanzu, ba gwamnati ba,” in ji wani manomi da ya rasa matsuguni.
Yayin da yawan wadanda aka sace ya haura 150 cikin kwanaki hudu, gonaki sun lalace, kuma amana ga gwamnati ta dusashe, matsalar tsaro a Zamfara na kara tabarbarewa.
Masu zanga-zangar sun ce ba za su bar fadar gwamnati ba sai sun ji amsa mai gamsarwa daga mahukunta ba alkawari ba, amma matakin gaske da zai dawo da tsaro a gidajensu.
“Ba mu zo nan domin tada hankali ba. Mun zo domin babu abin da ya rage mana babu tsaro, babu mazajenmu, babu yayammu,” in ji wata dattijar mata tana rike da jariri. “Muna roko. Don Allah ku taimaka mana?”
