Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyarta na gina layin dogon jirgin kasa mai sauƙi (light rail) a cikin birnin Kano, wanda zai ci kuɗi har naira tiriliyan 1.5. Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Wakilai, Hon. Abubakar Kabir Bichi ne ya bayyana haka.
Yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a Kano, Hon. Bichi ya ce aikin zai taimaka matuƙa wajen sauƙaƙa matsalolin sufuri a cikin birnin Kano.
Ya ce: “Aikin layin dogon jirgin kasa a cikin birnin Kano yana da kimanin dala biliyan 1, wanda yake daidai da naira tiriliyan 1.5, kuma shirye-shirye sun yi nisa don fara aiwatar da shi.”
“Wanda ya taɓa yin tafiya zuwa ƙasashen Turai ko Asiya ya san irin waɗannan ayyuka da yadda suke taimakawa. Wannan aiki zai ƙara daraja sosai ga tattalin arziƙin jihar idan an kammala shi,” in ji shi.
Hon. Bichi ya musanta jita-jitar cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya bada muhimmanci ga Arewacin Najeriya, yana mai cewa shugaban kasar ya kaddamar da muhimman ayyuka da dama a yankin, wanda suka haɗa da fannonin gine-gine, lafiya, noma, ilimi da tsaro.
“Abin dariya ne wasu su ce Shugaba Tinubu baya son wannan yanki. Ni ne shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar wakilai, kuma na san irin abubuwan da shugaban ya yi wa Arewa.”
“Ya kamata mu daina jinƙai ko nuna son zuciya, mu fadi gaskiya kan Shugaba Bola Tinubu. Shugaban ya kaddamar da manyan ayyuka a sassan Arewa daban-daban.”
Ya kuma kara da cewa, aikin titin Kaduna-Zaria-Kano na kusa da kammala.
Aikin titin Kaduna zuwa Abuja mai tsawon kimanin kilomita 400, an soke kwangilar da aka fara da ita, an kuma ba wani sabon kamfani wanda ya fara aiki. Bisa bayanin da na samu daga Ministan Ayyuka, aikin zai kammala kafin ƙarshen watanni ukun farko na shekara mai zuwa.
Har ila yau, akwai aikin titin Kano zuwa Hadejia mai tsawon kilomita 200 wanda an riga an kammala shi.
Hakanan akwai hanyar “Kano Northern Bypass” wadda ta ci kuɗi fiye da naira biliyan 250.
Dan majalisar ya ce sun ziyarci Kano ne domin taron shugabannin jam’iyyar APC a jihar, don tsara dabarun siyasa gabanin babban zaɓen 2027.
“A zaɓen da ya gabata, Kano ta bai wa Shugaban kasa Bola Tinubu ƙuri’u sama da 500,000 – mafi yawa a duk faɗin ƙasar nan. Don haka muna son fara shiri tun da wuri domin babban zaɓen 2027.”
“Taron kuma dama ce ta nuna goyon baya ga Dr. Abdullahi Umar Ganduje. Mutum ne da ya taka rawa sosai lokacin da yake Shugaban Jam’iyyar APC ta ƙasa. Ya samu nasarar karɓo jihohi da dama daga hannun PDP zuwa APC,” in ji shi.
