Yaki da HIV, TB: Global Fund Ta Ware Naira Tiriliyan 1.16 a Najeriya

Kungiyar Global Fund ta ware kimanin naira tiriliyan 1.16 (dala miliyan 790) domin tallafawa kokarin Najeriya na yaki da cututtukan HIV, tarin fuka (TB), da zazzabin cizon sauro, tare da karfafa tsarin kiwon lafiya daga shekarar 2027 zuwa 2029.

A karkashin wannan shiri, ana sa ran Najeriya za ta bayar da kaso 15 cikin 100 na kudaden a matsayin gudunmawar hadin gwiwa, bisa sharuddan sabon zagayen tallafin Global Fund na bakwai (Grant Cycle 7). Kungiyar ta yi gargadin cewa duk wani tsaiko a kudaden yaki da cutar TB na iya rusa nasarorin da aka samu a baya.

Jagoran tawagar Global Fund a Najeriya, Jean-Thomas Nouboussi, ya bayyana cewa yawan masu samun maganin TB ya karu daga mutum 100,000 a shekarar 2019 zuwa 458,000 a shekarar 2025, tare da samun nasarar jinya kusan kashi 90 cikin 100, lamarin da ya sanya shirin TB na Najeriya cikin mafi karfi a duniya.

Ya ce, “Ci gaba da wadannan nasarori na bukatar cikakken daukar nauyi daga gwamnati da kuma tabbatar da samar da kudade ba tare da tangarda ba.”

Nouboussi ya kuma bayyana fara amfani da allurar kariya daga HIV mai daukar lokaci mai tsawo, wato Lenacapavir (LEN) PrEP, a matsayin wani babban ci gaba. Ana sa ran Najeriya za ta karbi allurai 179,700 a cikin wani shiri na kai wa mutane miliyan biyu kariya zuwa shekarar 2028 a kasashe tara.

Ministan Lafiya na Jiha, Iziaq Adekunle Salako, ya ce rahoton masu dauke da cutar TB ya karu daga 130,591 a shekarar 2020 zuwa 440,000 a shekarar 2025, sakamakon fadada hanyoyin gano cutar kamar na’urorin GeneXpert, wadanda suka karu daga guda 32 a shekarar 2012 zuwa 527 a fadin kasar.
Ya kara da cewa cibiyoyin jinyar TB sun karu daga 39 a shekarar 2013 zuwa 372, yayin da nasarar jinya ta kai kashi 94 cikin 100.

Game da HIV, Salako ya ce Najeriya na gab da cimma burin UNAIDS na 95-95-95, inda kashi 93 cikin 100 na mutane suka san matsayinsu, kashi 99 cikin 100 suna karbar magani, yayin da kashi 95 cikin 100 suka samu raguwar kwayar cutar a jikinsu.

Haka kuma, shirin hana yaduwar cutar daga uwa zuwa jariri (PMTCT) ya inganta daga kashi 33 cikin 100 a shekarar 2023 zuwa kusan kashi 70 cikin 100 a shekarar 2025.

Ministan Lafiya mai kula da harkokin tsari, Muhammad Ali Pate, ya jaddada muhimmancin amfani da kudade yadda ya kamata a daidai lokacin da ake fama da karancin tallafin duniya.

Ya bayyana cewa sama da kashi 90 cikin 100 na kudaden kiwon lafiyar Najeriya daga cikin gida suke, wanda ke nuna bukatar kirkire-kirkire da kuma dorewar tsare-tsare.

Pate ya ce Najeriya ta samu gagarumin ci gaba a yaki da HIV, TB da zazzabin cizon sauro cikin shekaru 25 da suka gabata, amma sabbin kalubale na duniya na bukatar sabbin dabaru domin ci gaba da wannan nasara.