Kamfanonin rarraba wutar lantarki a Najeriya (DisCos) sun tara kuɗi har ₦204.74 biliyan a watan Janairu 2026, wanda ke nuna kashi 76.34% na karɓar kuɗaɗe, amma duk da haka sun yi asarar sama da ₦131 biliyan sakamakon gibi a lissafi da karɓar kuɗi.
Hukumar Nigerian Electricity Regulatory Commission (NERC) ta bayyana cewa kwastomomi sun kasa biyan kuɗin wuta har ₦63.46 biliyan, yayin da matsalolin tsarin harkar wuta gaba ɗaya suka haifar da babban gibin kudaden shiga.
Rahoton “Commercial Performance Factsheet” na Janairu 2026 ya nuna cewa daga cikin wutar lantarki da aka karɓa mai darajar ₦336.43 biliyan, an yi lissafin ₦268.20 biliyan ne kawai, wanda ke nuna ingancin lissafi na kashi 79.72%. Kuɗin da aka karɓa a zahiri ya tsaya ne a ₦204.74 biliyan.
NERC ta ce duk da cewa matsakaicin kuɗin wuta da aka amince da shi ya kai ₦124.30 a kowace kWh, a zahiri ana karɓar kusan ₦85.97 a kowace kWh, wanda ya haifar da ingancin dawo da kuɗi na kashi 69.16%—raguwar maki 8.1 idan aka kwatanta da watan Disamba 2025.
Ayyukan kamfanonin sun bambanta sosai, inda kamfanin rarraba wuta na Eko ya jagoranta da kashi 87.92% na dawo da kuɗi, sai Ikeja Electric da kashi 81.64%.
Kamfanonin Abuja da Fatakwal sun samu kusan kashi 75%, yayin da Kaduna da Jos suka yi ƙasa da hakan da kashi 36.29% da 43.54% bi da bi.
Hukumar ta nuna damuwa kan ci gaba da asarar ATC&C (fasaha, kasuwanci da karɓar kuɗi), inda kamfanoni masu ƙarfi kamar Eko da Ikeja ke da ƙananan asara, yayin da Jos, Kaduna da Yola ke fama da manyan matsaloli da satar wuta.
Domin inganta aiki, NERC ta amince da rage adadin asarar ATC&C na shekarar 2026 zuwa matsakaicin kashi 16.92% daga kashi 20.54% a 2025. Kamfanin Yola ne ya samu mafi girman ragin, daga kashi 44% zuwa 29%.
Duk da waɗannan gyare-gyare, sakamakon watan Janairu bai kai yadda ake fata ba, wanda ke nuna ci gaba da matsalar ƙarancin kuɗi a bangaren wutar lantarki.
NERC ta ce rage gibi tsakanin wutar da ake bayarwa da kuɗin da ake karɓa yana da matuƙar muhimmanci wajen daidaita kasuwar wutar lantarki a Najeriya.
