Kamfanin Nigerian National Petroleum Company Limited (NNPCL) ya bayyana cewa samar da danyen mai a Najeriya ya karu daga mafi ƙanƙanta na ganga 960,000 a rana a shekarar 2022 zuwa matsakaicin ganga miliyan 1.71 a rana, inda ya kai kololuwa na ganga miliyan 1.84 a shekarar 2025, sakamakon ƙarfafa tsaron bututun mai a yankin Neja Delta.
Babban Jami’in Gudanarwa na kamfanin, Bashir Bayo Ojulari, ne ya bayyana hakan a wani taron majalisa kan tsaron bututun mai da aka gudanar a Abuja. Ya ce an samu wannan nasara ne ta hanyar matakan gwamnati na kare muhimman kayayyakin mai.
Ojulari ya bayyana cewa nasarar ta samo asali ne daga haɗa kai tsakanin bangarori daban-daban, ciki har da haɗin gwiwar majalisa da zartarwa, tattara sahihan bayanai, tura jami’an tsaro, kulawar hukumomi, haɗin kan masana’antu, da kuma sa ido daga al’umma.
Ya ce yaƙi da satar mai da lalata bututun mai ya taimaka wajen dawo da amincewar masu zuba jari a bangaren mai da iskar gas na Najeriya.
A nasa ɓangaren, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, wanda Jimoh Ibrahim ya wakilta, ya bukaci a ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomi. Haka kuma, Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, wanda Julius Ihonvbere ya wakilta, ya buƙaci masu ruwa da tsaki su ci gaba da tantance ci gaban da aka samu domin tabbatar da adalci.
Taron ya samu halartar hukumomin tsaro da dama ciki har da sojoji, ’yan sanda, DSS da NSCDC, tare da kamfanoni masu zaman kansu, inda aka bayyana hanyoyin tsaro masu matakai daban-daban na kare bututun mai.
Bayanin Ojulari ya zo ne kwanaki kaɗan bayan Nigerian Upstream Petroleum Regulatory Commission (NUPRC) ta tabbatar da cewa samar da mai ya kai ganga miliyan 1.84 a watan Maris, daga ganga miliyan 1.4 a watan Fabrairu, lokacin da gyaran wasu matatun mai ya rage yawan samarwa.
NNPCL ta ce ingantaccen tsarin tsaro shi ne ginshiƙi wajen ci gaba da ƙara yawan samar da mai da kuma daidaita kudaden shiga na Najeriya daga man fetur.
