Ƙungiyar Likitocin Gida ta Najeriya (NARD) ta yi gargadin cewa duk wani yunƙuri na soke Tsarin Albashin Ƙwararru (PAT) na barazana ga jin daɗin likitoci, kuma zai iya jefa tsarin kiwon lafiya cikin matsala.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na ƙungiyar, Dakta Abdulmajid Ibrahim ya sanya wa hannu, NARD ta bayyana wannan mataki a matsayin “rashin adalci” wanda zai iya haifar da damuwa ga mambobinta.
Gargadin ya biyo bayan wata ganawa da shugabannin NARD suka yi da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, wadda suka bayyana a matsayin ganawa mai matuƙar muhimmanci da tasiri kan jin daɗin likitoci.
Tun da farko, NARD ta ayyana yajin aiki na ƙasa baki ɗaya ba tare da wa’adi ba a ranar 7 ga Afrilu, 2026, sakamakon shirin gwamnati na dakatar da aiwatar da sabon tsarin PAT, wanda ya kasance cikin yarjejeniyar da aka cimma bayan yajin aikin 2025.
Sai dai bayan ‘yan sa’o’i kaɗan da fara yajin aikin, ƙungiyar ta dakatar da shi, tare da bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin makonni biyu domin magance sauran matsalolin da suka haɗa da rashin biyan wasu alawus-alawus da kuma Asusun Horar da Likitocin Gida na shekarar 2026.
Dakatar da yajin aikin ya biyo bayan sa hannun Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima, Ministan Lafiya, Muhammad Pate, da sauran masu ruwa da tsaki. NARD ta kuma buƙaci mambobinta da su kasance cikin natsuwa da haɗin kai yayin da shugabanninta ke ci gaba da tattaunawa da gwamnati.
Sanarwar ta ce: “Muna nan daram, muna aiki tukuru, kuma ba za mu ja da baya ba wajen kare haƙƙoƙinku da inganta jin daɗinku.”
A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima ya tabbatar wa likitocin cewa ba za a soke PAT ba.
Ya ce: “PAT ya riga ya zama doka. Babu wanda zai soke abin da aka riga aka aiwatar a matsayin haƙƙinku na halal da kuka cancanta,” tare da alƙawarin cewa za a magance sauran buƙatun bayan kammala tsarin kasafin kuɗi.
NARD ta sake jaddada aniyarta na kare muradun likitocin gida da kuma inganta yanayin aikinsu, tana mai cewa haɗin kai da jajircewa su ne mabuɗin samun makoma mai kyau ga mambobinta.
