Tinubu ya Nada Farfesa Segun Aina a Matsayin Sabon Magatakardar JAMB

Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da nadin Farfesa Segun Aina a matsayin sabon Magatakardar Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta Kasa, Joint Admissions and Matriculation Board (JAMB).

Aina zai maye gurbin Farfesa Ishaq Oloyede, wanda wa’adin aikinsa zai kare a ranar 31 ga watan Yulin 2026.

Sanarwar nadin na kunshe ne a cikin wata takarda da mai bai wa shugaban kasa shawara kan yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Alhamis.

Sanarwar ta bayyana cewa Farfesa Aina malami ne a fannin Injiniyan Kwamfuta a Obafemi Awolowo University da ke Ile-Ife, kuma yana da kwarewa sosai a bangaren tsarin fasahar dijital, gudanar da jarabawa da sauye-sauyen hukumomin gwamnati.

Ta kuma bayyana shi a matsayin gogaggen masani kuma kwararre a tsarin gudanarwa, wanda ya shafe sama da shekaru 15 yana bai wa gwamnatocin tarayya da jihohi shawara kan sauyin fasahar zamani, gyaran tsare-tsare da kuma kare sahihancin jarabawa.

“Farfesa Aina, wanda zai cika shekaru 40 a watan Yuli, fitaccen masani ne kuma kwararre a tsarin gudanarwa da ke da gogewa sosai a tsarin jarabawar kasa, fasahar dijital da sauye-sauyen hukumomin gwamnati,” in ji sanarwar.

Fadar Shugaban Kasa ta ce sabon magatakardar yana da digirin farko a fannin Computer Systems Engineering daga University of Kent, sannan yana da digirin digirgir a Internet Computing da Network Security, da kuma PhD a Digital Signal Processing daga Loughborough University.

Haka kuma ya halarci shirin horar da manyan jami’ai a Lagos Business School.

Sanarwar ta kara da cewa Aina ya yi aiki a matsayin mai ba da shawara ga hukumomin shirya jarabawa da dama ciki har da National Examinations Council (NECO) da National Business and Technical Examinations Board (NABTEB), musamman kan tsarin ICT da kare sahihancin jarabawa.

An kuma bayyana cewa shi mamba ne na kungiyoyi masu zaman kansu da suka hada da Nigerian Society of Engineers, da Institute of Electrical and Electronics Engineers (IEEE), da kuma Council for the Regulation of Engineering in Nigeria.

Shugaba Tinubu ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa sabon Magatakardar JAMB zai ci gaba da inganta sauye-sauye da nasarorin da aka samu karkashin jagorancin Oloyede, tare da kai hukumar zuwa wani sabon mataki na inganci da kirkire-kirkire.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *