Wani sabon bincike daga PAC Research ya bayyana cewa Najeriya na bukatar kusan sabbin gidaje 800,000 a kowace shekara domin ci gaba da biyan bukatun karuwar yawan jama’a.
Rahoton ya kuma yi hasashen cewa bukatar gidaje na iya kaiwa gidaje miliyan 2 a kowace shekara zuwa shekarar 2030, abin da ke nuna girman matsalar karancin gidaje a kasar.
Rahotannin biyu mai taken “From Shortage to Opportunity: Unlocking the Billion-Dollar Housing Market” da “Lagos Housing Report: A Treasure Trove of Possibilities” sun kiyasta cewa Najeriya na da gibin gidaje da ya kai kusan miliyan 28, yayin da jihar Lagos ita kadai ke da gibin gidaje kusan miliyan 3.4.
Duk da wannan matsala, rahoton ya bayyana cewa gibin na iya zama babbar damar zuba jari, inda darajar kasuwar gidaje a Najeriya ke kaiwa tiriliyoyin naira.
Rahoton ya kuma nuna cewa karɓar lamunin gidaje (mortgage) a Najeriya ya yi kasa sosai, inda bai kai kashi 1% na GDP ba, idan aka kwatanta da kashi 77% a Amurka da kashi 31% a Afirka ta Kudu.
Rahoton kasa baki daya ya ce: “Najeriya na cikin wani muhimmin lokaci da saurin bunkasar birane da sauye-sauyen tattalin arziki ke haduwa domin samar da damammaki masu yawa.”
A jihar Lagos, wadda ke karɓar sabbin mazauna kusan 475,000 a kowace shekara, rahoton ya nuna cewa gidajen da ake da su sun kai miliyan 1.49, yayin da bukata ke kusan miliyan 4.69, wanda ke haifar da gibin gidaje miliyan 2.81.
Fiye da kashi 52% na mazauna Lagos sun fi son gidajen daki daya ko biyu, abin da ke nuna bukatar gidaje masu sauki da araha. Haka kuma, hayar gidaje a yankunan da suka fi tsada kamar Victoria Island na iya kaiwa har ₦18 miliyan a shekara.
Rahoton ya ba da shawarar samar da gidaje a matakai (incremental housing), kara samun damar lamunin gidaje, da kuma karfafa hadin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu (PPPs) domin magance gibin.
Shugaban Darakta Janar na Federal Mortgage Bank of Nigeria, Shehu Usman Osidi, ya bayyana sakamakon binciken a matsayin “kira zuwa aiki,” yana mai cewa yanzu ne lokacin da ya dace a zuba jari a bangaren gidaje a Najeriya.

