Taron Abuja Economic Dialogue Ya Nuna Hanyoyin Farfaɗo da Tattalin Arzikin Nigeria

Masu tsara manufofi, shugabannin kamfanoni, kwararrun masana tattalin arziki da abokan ci gaban kasa sun bayyana cewa Nigeria na bukatar ɗaukar ƙarin matakai na aikace-aikace domin tabbatar da dorewar ci gaba da inganta tattalin arziki.

Sun bayyana hakan ne a wajen ƙaddamar da Ignite Nigeria Economic Outlook 2026 da aka gudanar a Fraser Suites, Abuja, ranar Laraba.

Taron, wanda Ignite Capital Ltd da Abuja Economic Dialogue suka shirya, ya gudana ne a ƙarƙashin taken “Navigating Growth, Capital and Reform.”

A jawabin bude taro, Kyari Abba Bukar, wanda ya assasa Abuja Economic Dialogue kuma shi ne shugaban Ignite Capital, ya ce lokaci ya yi da Nigeria za ta daina takaita kai ga manufofi kawai, ta koma ga aiwatar da su cikin tsari mai dorewa.

Ya ce, “Dole mu sauya daga manufofi zuwa aiwatarwa mai karfi da tasiri. Abuja Economic Dialogue na da niyyar gina tattaunawa bisa bayanai tsakanin gwamnati da ‘yan kasuwa. Muna bukatar ƙirƙira da tallafa wa irin waɗannan muƙamai.”

A nasa jawabin, tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Arc. Namadi Sambo (GCON), ya yaba da rahoton Outlook saboda zurfin bincikensa, sannan ya jaddada bukatar inganta manyan sauye-sauyen tattalin arziki da Nigeria ta fara.

Ya ce Nigeria na tsaye a mahangar tarihi wadda ke tattare da kalubale masu yawa da kuma damar ci gaba mai yawa.

Sambo ya jaddada muhimman batutuwa biyar da rahoton ya fi karkata zuwa gare su:

  1. Inganta ƙarfin samarwa da sauya tsarin tattalin arziki
  2. Gyaran wutar lantarki da ababen more rayuwa
  3. Fasaha da tattalin arzikin dijital
  4. Kasuwanci cikin Afrika karkashin AfCFTA
  5. Tsaro, tsarin abinci da kariyar jama’a

Ya kuma yabawa gwamnati, musamman wajen cigaban da ake samu a harkar samar da wutar lantarki da nasarar kammala wasu sabbin tashoshin wutar lantarki masu motsi.

Sambo ya kara da cewa, “Nigeria ta samu cigaba a bangaren gyaran harkar canjin kudade, raguwar hauhawar farashi, ci gaban ayyukan dijital da kuma karuwar ajiyar kasashen waje. Amma dole ne mu hanzarta aiwatar da ƙarin gyare-gyare, mu zuba jari a makamashi mai sabuntawa, mu fadada kasuwanci a yankin Afrika, kuma mu ƙarfafa tsarin tsaro.”

A nasa bangaren, tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Dr. Bukola Saraki, ya gargadi cewa duk wani gyaran tattalin arziki dole ne ya canza rayuwar al’umma kai tsaye.

Ya ce, “Tambayar ba ko gyara ya dace ba—ya dace. Amma shin wadannan matakai za su fassara zuwa ci gaban da jama’a za su ji a rayuwarsu ta yau da kullum?”

Shi ma Dr. Paul Arinze, shugaban Pedestal Africa, ya gabatar da nazarin tattalin arzikin 2025 da kuma hasashen 2026, inda ya bayyana sabbin yanayi uku da tattalin arzikin Nigeria ka iya tsayawa a 2026:

  1. Yanayin Ci gaba (Upside Scenario):
    GDP ya kai 4.7%–5.1%, ta hanyar ingantaccen tsaro a yankunan noma, sauƙaƙan gyare-gyaren wutar lantarki, ƙarin zuba jari, da haɓakar samar da mai.
  2. Yanayin Daidaituwa (Baseline Scenario):
    GDP 4.0%–4.2%, inda hauhawar farashi ke sauka zuwa 19–20%, kasuwar FX ta daidaita, da cigaban bangaren ayyuka.
  3. Yanayin Faduwa (Downside Scenario):
    GDP 2.3%–2.7%, idan farashin mai ya girgiza, FX ta sake tabarbarewa, tsaro ya ƙara muni ko kuma dangantakar kasashen waje ta matse.

An rufe taron da tattaunawa mai zurfi da Fahad Garba Aliyu ya jagoranta, tare da manyan masana tattalin arziki kamar:

● Dr. Sarah Alade – Tsohuwar Mataimakiyar Gwamnan CBN
● Dr. Umaru Kwairanga – Shugaban NGX Group
● Dr. Nurudeen Zauro – Mai ba shugaban kasa shawara kan hada-hadar tattalin arziki
● Yanmo Omorogbe – COO, Bamboo