Ministan kirkire-kirkire, kimiyya da fasaha, Uche Nnaji, ya yi murabus daga mukaminsa bayan zarge-zargen bogin takardun karatu da ake yi masa.
Nnaji ya shiga cikin rikici bayan zargin cewa ya mika takardun karatu na jabu ga Shugaba Bola Tinubu da kuma majalisar dattawa lokacin tantancewar ministoci.
Binciken da jaridar PREMIUM TIMES ta gudanar ya gano cewa Nnaji bai kammala karatunsa a jami’a ba, sannan takardar digiri da takardar hidimar kasa (NYSC) da ya gabatar ga Shugaba Tinubu, ofishin sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Hukumar Tsaron Cikin Gida (DSS), da majalisar dattawa, duk bogi ne.
Karin bayani zai biyo baya…





