Ministan Kirkire-kirkire, Kimiyya da Fasaha, Chief Uche Geoffrey Nnaji, ya yi murabus daga mukaminsa, yana mai cewa matsin lamba da kuma kai hare-haren karya da ake yi masa a kafafen yada labarai ne ya sa ya yanke wannan shawarar.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, Nnaji ya bayyana cewa, “Wannan shawara ba ta zo da sauƙi ba. A cikin makon da ya gabata, an kaddamar da wata manufa ta kai hare-haren karya, na siyasa, da kuma kazafi a kaina, da mutuncina, da ofishina — ta kafafen jaridu, rediyo, talabijin, da kafafen sada zumunta.”
Ya ce duk wadannan zarge-zargen ba su da tushe kuma manufarsu ita ce su karkatar da hankali daga muhimman ayyukan ma’aikatarsa.
“Wadannan zarge-zargen marasa tushe da kuma rahotannin bogi sun jawo min damuwa ta kaina, kuma sun fara janyo cikas ga muhimman ayyukan ma’aikata da kuma shirye-shiryen Renewed Hope na shugaban kasa,” in ji shi.
Nnaji ya kara da cewa murabus dinsa ba alamar amincewa da laifi ba ne, illa kawai wata hanyar mutunta tsarin shari’a da kare amincin shari’ar da ke gaban kotu.
“Shawarata ta janye kaina daga mukami shawara ce ta kaina, ba don na amince da wani laifi ba, amma don mutunta tsarin shari’a da kuma kare mutuncin shari’ar da ke gaban kotu,” in ji shi.
Tsohon ministan ya gode wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu bisa damar da ya ba shi na yin hidima a gwamnatinsa, tare da tabbatar da goyon bayansa ga manufofin gwamnatin.
“Ina matukar gode wa Mai Girma Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, saboda amincewar da ya nuna a kaina da kuma damar da ya ba ni na yin aiki a cikin majalisar ministoci.
“Manufarsa ta ganin Najeriya ta zama kasa mai kirkire-kirkire, ci gaban fasaha, da sabbin dabaru tana da muhimmanci a wurina, kuma ina tabbatar da cikakken goyon bayana ga gwamnatin sa da manufofin ta na sauyi,” in ji Nnaji.





